Kungiyar ƙwadago ta buƙaci tallafin gaggawa ga ma’aikata bayan tashin farashin fetur

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kungiyar ƙwadago ta Nijeriya (NLC), ta yi kira cikin gaggawa ga Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki matakan rage radadin tsadar rayuwa da ke ƙara ta’azzara sakamakon tashin farashin man fetur a ƙasar.

ƙungiyar ta buƙaci a samar da ƙarin alawus na tsadar rayuwa ga ma’aikata, kyautar ƙarin albashi na wucin gadi, sassaucin haraji, da kuma ɗaukar matakan gaggawa domin farfaɗo da matatun mai na gwamnati.

NLC ta bayyana cewa sabon farashin man fetur, wanda yanzu ke tsakanin naira 1,170 zuwa 1,300 a lita, ya ƙara jefa ma’aikata da talakawan kasa cikin mawuyacin hali na tattalin arziki.

Shugaban NLC, Joe Ajaero, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa mai taken “Ceto ‘Yan Nijeriya Daga Wannan Kaɗuwa: Taimakon Gaggawa Ya Zama Dole,” wadda aka samu a Abuja.

Ya ce ƙungiyar na isar da koke-koken miliyoyin ma’aikatan Nijeriya da ke shan wahala sakamakon rikicin tattalin arzikin duniya da ba su jawo ba.

A cewarsa, tashin hankali da yaƙin da ke tattare da Amurka da Isra’ila da Iran ya girgiza kasuwannin mai na duniya, lamarin da ya haddasa tashin farashin mai a Nijeriya.

Ya ƙara da cewa, yayin da manyan ƙasashe ke fafatawa a fagen siyasa da soja, talakawan Nijeriya ne ke shan azaba ta hanyar talauci da yunwa, saboda gazawar tabbatar da cewa matatun mai na gwamnati suna aiki yadda ya kamata.

NLC ta ce wannan rikici ya nuna raunana tsarin bangaren rarraba man fetur na ƙasar, tare da karya hasashen cewa tace mai a gida kaɗai zai kare Nijeriya daga tasirin sauye-sauyen farashi a kasuwar duniya. ƙungiyar ta kuma yi nuni da cewa matatar Dangote ma ta daidaita farashinta bisa sauyin kasuwar duniya, abin da ya ƙara jefa nauyi kai tsaye kan talakawa.

ƙungiyar ta yi gargadin cewa muddin Nijeriya na dogaro da tsarin farashi da kasuwa ke tantancewa wanda ke karkashin tasirin duniya, kuma ba ta farfaɗo da matatun mai na gwamnati ba, to ƙasar za ta ci gaba da zama cikin haɗarin tasirin rikice-rikicen ƙasa da ƙasa da kuma hasashen kasuwa.

Ta kuma jaddada buƙatar a gyara tare da mayar da matatun mai na Fatakwal, Warri da Kaduna cikakkiyar aiki, tana mai cewa hakan hakki ne na ‘yan Nijeriya, ba wata alfarma ba. NLC ta ce ba wata kasa da za ta samu ‘yancin tattalin arziki idan tana fitar da ayyukan yi zuwa waje sannan tana shigo da tsadar kayayyaki daga ƙasashen waje.

ƙungiyar ta nuna cewa tashin farashin fetur da dizel ya sa sufuri ya zama babban nauyi ga ma’aikata, yayin da hauhawar farashin abinci ke kara lalata ƙaramin albashi. Ta yi gargaɗin cewa idan ma’aikata ba za su iya biyan kuɗin zuwa wurin aiki ba, tattalin arziki zai tsaya cik; idan kuma iyalai ba za su iya cin abinci sau uku a rana ba, al’umma za ta shiga haɗari.

NLC ta kuma yi kira da a faɗaɗa shirin tallafin kuɗin kai tsaye ga talakawa tare da tabbatar da gaskiya wajen rarraba shi, tare da daidaita kuɗin tallafin bisa hauhawar farashin kaya. Haka kuma ta buƙaci sassauta haraji ga ma’aikata, musamman masu ƙaramin ƙarfi, tana mai cewa karɓar haraji daga masu karamin albashi ya yi kama da zalunci.

ƙungiyar ta yi nuni da hasashen da Nigeria Economic Summit Group (NESG) ta fitar cewa Nijeriya na iya samun ribar kudin mai har naira tiriliyan 30 sakamakon rikicin Gabas ta Tsakiya. NLC ta ce dole ne a zuba irin wadannan kudade wajen taimaka wa jama’a maimakon su ɓace kamar yadda ya faru a baya.

A ƙarshe, NLC ta buƙaci gwamnati ta bude tattaunawa ta gaskiya da ma’aikata da jama’a, tana mai cewa bai dace a yi amfani da rikicin waje a matsayin uzuri na manufofin da ke ƙara talauci ba. Ta jaddada cewa babban nauyin gwamnati shi ne kare jin daɗin rayuwa da tsaron ‘yan ƙasa, tare da kira ga daukar mataki cikin gaggawa domin tabbatar da adalci da rayuwar jama’a.

By ukarofi