Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnan Jihar Anambra, Chukwuma Soludo, ya sake karɓar rantsuwa domin fara wa’adi na biyu a kan kujerarsa.
Haka kuma, mataimakinsa Onyekachukwu Ibezim ya sake karɓar rantsuwa domin sabon wa’adi a matsayin mataimakin gwamna.
Soludo ya samu nasara a zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar a watan Nuwamban 2025, inda ya kada babban abokin hamayyarsa Nicholas Ukachukwu na Jam’iyyar APC.
An gudanar da bikin rantsuwar ne a ranar Talata a birnin Awka, babban birnin jihar, tare da halartar manyan baƙi daga sassa daban-daban.
Daga cikin waɗanda suka halarta akwai mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, da tsoffin shugabannin ƙasa Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan.
Bikin ya kuma samu halartar manyan ‘yan siyasa, jami’an gwamnati, magoya baya da kuma sarakunan gargajiya, wanda ke nuna fara sabon wa’adi na shekaru huɗu ga gwamnan.
A cikin jawabin da ya gabatar bayan rantsuwa, Soludo ya yi alƙawarin cika dukkan alƙawuran da ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe.
Ya bayyana cewa sake zaɓensa wata gagarumar amincewa ce da manufofinsa, yana mai jaddada cewa ba za su ɗauki goyon bayan al’ummar jihar da wasa ba.
