Ƙananan hukumomi 32 na Kano sun kuɓuta daga matsalar bahaya a fili, inji ƙwararru

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Shugaban tawagar tsarin wanke hannu don lafiya wato (WASH Systems for Health) na ƙungiyar Self Help Africa, Timothy Ibeawuchi, Ya bayyana cewa, bisa tsarin kamfen din “Clean Nigeria”, Jihar Kano ta samu gagarumin ci gaba inda ya ce ƙananan hukumomi 32 daga cikin 44 na jihar tuni aka ayyana su a matsayin waɗanda suka kawar da yin bahaya a fili, wato (Open defecation free)

A cewarsa, jihar na ci gaba da ɗaukar wani sabon mataki ta hanyar samar da cikakken tsari mai ɗorewa na tsaftar muhalli, wanda zai tabbatar da samar da ayyukan tsafta masu inganci, kuma masu ɗorewa da daidaito ga kowa.

Sannan ya yaba wa Gwamnatin Jihar Kano bisa ƙoƙarin da take yi a bangaren tsaftar muhalli.

Timothy ya bayyana hakan ne yayin gabatar da sakamakon wani taron bita na kwanaki biyu na masu ruwa da tsaki kan samar da tsarin samun ɗorewar tsaftar muhalli, wanda Self Help Africa ta shirya tare da tallafin Gwamnatin Jihar Kano a Kaduna ranar Alhamis.

A nasa jawabin, babban sakataren ma’aikatar albarkatun ruwa ta Jihar Kano, Injiniya Abdulrazaq Haruna, ya sake jaddada ƙudirin Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf na samar da muhimman ayyukan jin ƙai ga al’umma, musamman a ɓangaren ruwa, tsafta da kiwon lafiya wato (WASH).

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar na ci gaba da haɗa hannu da masu ruwa da tsaki domin samar da wani tsari mai ɗorewa kuma mai jure sauyin yanayi, wanda zai tabbatar da cewa kowa ya samu damar cin gajiyar ayyukan tsaftar muhalli.

Injiniya Abdulrazaq ya kuma yaba da irin gudunmawar da mahalarta taron suka bayar, tare da ƙarfafa musu gwiwa da su ci gaba da bayar da shawarwari masu amfani domin samar da takardar da za ta yi tasiri mai kyau ga rayuwar al’ummar jihar Kano.

Shi kuwa mashawarci a harkokin tsabtace muhalli da haɗin gwiwa, Sukumun N. Ezekiel, cewa ya yi ƙananan hukumomi 170 ne kacal daga cikin 774 da ake da su a Nijeriya aka ayyana a matsayin waɗanda suka kawar da yin bahaya a fili.

Ya ce wannan adadi na nuna irin ci gaban da aka samu zuwa yanzu, tare da kuma jaddada buƙatar ƙara ƙaimi wajen ganin an kawo ƙarshen matsalar yin bahaya a fili a faɗin kasar nan cikin ‘yan shekaru masu zuwa.

Da take jawabi a madadin mahalarta taron, Ambasada Rabi Yusuf Gezawa ta yaba wa Gwamnatin Jihar Kano da kuma Self Help Africa bisa ba su damar bada gudunmawa wajen samar da wannan tsari.

Ta ƙara da cewa haɗa masu buƙata ta musamman cikin wannan tsari tun daga matakin farko na nuna cewa an bai wa batun haɗa kowa da kowa muhimmanci tun kafin kammala wannan kundi.

Taron dai ya samu halartar wakilai daga ma’aikatu, hukumomi, makarantu da kuma ƙungiyoyi daga sassa daban-daban na jihar Kano sama da 30, tare da abokan hulɗa na ci gaba da sauran masu ruwa da tsaki.

By ukarofi