Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Babban Sufeton ’Yan Sandan Nijeriya (IGP), Olatunji Disu, ya amince da wani gagarumin sauyi a cikin Rundunar ’Yan Sandan ƙasa, inda aka sake rarraba manyan jami’ai zuwa sabbin wuraren aiki domin ƙarfafa tsarin tsaro da inganta gudanarwa.
Wannan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar ’Yan Sanda, Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda (DCP), Anthony Placid, ya fitar, inda ya bayyana cewa matakin wani ɓangare ne na ƙoƙarin rundunar na ƙarfafa jagoranci, haɓaka aiki, da kuma inganta hidima ga al’umma a faɗin ƙasar.
Sanarwar ta jaddada cewa sauyin ya yi daidai da manufar rundunar na tabbatar da ingantaccen tsarin jagoranci da kuma yadda ake tura jami’ai bisa tsari a sassa daban-daban, ciki har da rundunoni, ofisoshi da kuma sassan aiki.
A cikin sabon tsarin, Mataimakan Sufetocin ’Yan Sanda (AIG) da dama sun samu sabbin muƙamai. Daga ciki akwai AIG Ado Emmanuel da aka tura Sashen Bincike da Tsare-tsare a Hedikwatar Rundunar da ke Abuja, yayin da AIG Joseph Eribo zai jagoranci Sashen Makamai. Haka kuma, AIG Miller Dantawaye ya koma Sashen Ayyuka, sai AIG Henry Ifeanyi Uche da aka bai wa Sashen Horaswa da Ci-gaba.
Sauran sun haɗa da AIG Olanrewaju Peter Ogunlowo da aka tura Sashen Harkokin ’Yan Sanda, da AIG Dahiru Mohammed zuwa Yankin ’Yan Sanda na 15 da ke Maiduguri. Haka kuma AIG Dankombo Morris zai yi aiki a Yanki na 4 a Makurdi, yayin da AIG Bello Shehu zai jagoranci Yanki na 14 a Katsina.
A matakin Kwamishinonin ’Yan Sanda (CP), an tura CP Haruna Alaba Yahaya zuwa Jihar Jigawa, CP Olugbenga Abimbola zuwa Oyo, sai CP Olubode Ojajuni zuwa Ogun. Haka kuma, CP Michael Falade zai jagoranci Ekiti, yayin da CP Yakubu Dankaro aka tura Adamawa.
Babban Birnin Tarayya Abuja zai kasance ƙarƙashin jagorancin CP Muhammed Sanusi Ahmed, yayin da CP Olatunji Fatai zai kula da Jihar Legas. Sauran sun haɗa da CP Morkwap Dongshal (Taraba), CP Ahmed Bello (Zamfara), CP Umar Fagge (Katsina) da CP Hayatu Hassan (Sokoto).
Haka zalika, an yi wasu muhimman naɗe-naɗe a sassa na musamman, ciki har da INTERPOL, Sashen Kare Muhimman Mutane, Sashen Binciken Manyan Laifuka (FCID), da Kwalejin Horas da ’Yan Sanda (POLAC), domin ƙarfafa aikin rundunar a fannoni daban-daban.
A ƙarshe, Babban Sufeton ’Yan Sandan ya buƙaci sabbin jami’an da aka tura da su yi amfani da ƙwarewarsu da gogewarsu wajen gudanar da ayyukansu cikin ƙwarewa, ladabi da bin doka, domin tabbatar da tsaro da amincewar jama’a.
