Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Rundunar sojojin Nijeriya da ke ƙarƙashin shirin Operation Haɗin Kai ta cafke mutane 18 da ake zargi da safarar kayayyaki ga ’yan ta’addan Boko Haram a Jihar Borno.
Rahotanni sun bayyana cewa an kama waɗannan mutane ne yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa ƙaramar hukumar Gubio, inda daga nan suke shirin wucewa zuwa yankin Gudumbali, wuri da aka fi sani da mafakar ’yan ta’addan.
Bayanin kama su ya fito ne cikin rahoton ayyukan yau da kullum na rundunar, wanda aka bai wa Kamfanin Dillancin Labarai ta Nijeriya (NAN) a ranar Laraba.
Rahoton ya nuna cewa an cafke mutanen ne yayin da suke ɗauke da kayayyakin da ake zargin an tanadar su ne domin taimakawa masu tayar da ƙayar baya.
A binciken farko da aka gudanar, an gano cewa waɗanda ake zargin sun amsa laifinsu, inda suka bayyana cewa suna saye da kuma kai kayayyaki ga ’yan ta’addan a kai a kai.
Rahoton ya ce, “Sun amince cewa sukan sayo kayayyaki suna kai wa ’yan ta’addan. Sun kuma danganta hakan da rashin aikin yi, abin da ke nuna akwai babbar matsalar tattalin arziki a Maiduguri da kewaye.”
Rundunar sojin ta jaddada cewa wannan lamari ya ƙara tabbatar da maganganun Babban Hafsan Tsaron Nijeriya dangane da alaƙar da ke tsakanin matsin tattalin arziki da ci gaba da wanzuwar hanyoyin samar da kayayyaki ga ’yan ta’adda.
Haka kuma, rundunar ta bayyana cewa rawar da wasu fararen hula ke takawa wajen tallafa wa ayyukan ta’addanci na da matuƙar muhimmanci, musamman a yankunan karkara kamar Gubio da Gudumbali.
Sojojin sun buƙaci a ɗauki matakan da suka wuce na soja kawai, inda suka jaddada buƙatar haɗa dabarun tsaro da shirye-shiryen bunƙasa tattalin arziki da samar da ayyukan yi domin magance tushen matsalar ta’addanci.
Duk da cewa, a bara Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro a ƙasar, hare-haren ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane na ci gaba da faruwa a sassa daban-daban, lamarin da ke ƙara tayar da hankali a tsakanin al’umma.
