Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Ministan Ayyuka na Tarayya, Daɓid Umahi, ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta gaji bashin sama da Naira tiriliyan 13 tare da ayyukan tituna fiye da 268 da ake gudanarwa a faɗin ƙasar nan, zuwa ranar 29 ga Mayu, 2023.
Umahi ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin wata ziyara ta duba manyan ayyukan gine-gine a yankin Kudu maso Gabas, inda ya kai ziyara wuraren da ake gudanar da aikin gadar sama ta Abakpa Junction, gadar sama ta Eke-Obinagu, da kuma aikin gyaran babbar hanyar Enugu zuwa Onitsha.
Ya ce tun bayan karɓar mulki, gwamnatin yanzu ta ɗauki matakai masu ƙarfi domin farfaɗo da ayyukan da aka yi watsi da su tare da ƙaddamar da sabbin ayyuka a sassa daban-daban na ƙasar.
A cewarsa, kafin wannan gwamnati ta zo, yanayin titunan Nijeriya ya kasance cikin matsanancin lalacewa, inda direbobi ba sa iya tafiyar awa guda ba tare da cin karo da ɓangarorin tituna marasa kyau ba. Sai dai ya jaddada cewa halin na sauyawa sannu a hankali sakamakon matakan da gwamnati ke ɗauka.
“Mun gaji bashin da ya yi tsanani, sama da tiriliyan N13, tare da ayyuka sama da 268. A da ba za ka iya tafiya awa guda ba ba tare da ka gamu da mummunan titi ba, amma yanzu hakan na zama tarihi sakamakon abin da Shugaban ƙasa ke yi,” inji Umahi.
Ya ƙara da cewa, koke-koken ’yan Nijeriya kan lalacewar tituna na raguwa a hankali, duk da cewa ba za a iya gyara komai a lokaci guda ba. Duk da haka, ya tabbatar da cewa gwamnati na da niyyar samar da tituna da gadajen da za su daɗe suna amfani a ko’ina cikin ƙasar.
A wani mataki na rage wahalhalun zirga-zirga, ministan ya umarci a buɗe wani sashe mai tsawon kilomita 15 na hanyar Enugu zuwa Onitsha ga ababen hawa kafin ƙarshen watan Maris na shekarar 2026. Ya ce hakan zai sauƙaƙa zirga-zirga tare da ƙarfafa harkokin kasuwanci a yankin.
Umahi ya bayyana hanyoyin Enugu–Onitsha da Enugu–Fatakwal a matsayin muhimman hanyoyi da suka daɗe suna fama da cunkoso, haɗurran tankokin mai da kuma lalacewar tituna. Ya nuna ƙwarin gwiwa cewa ayyukan da ake yi yanzu za su magance waɗannan matsaloli gaba ɗaya.
Haka kuma, ministan ya yaba wa Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, bisa goyon bayan da yake bai wa ayyukan gwamnatin tarayya, musamman wajen biyan diyya da kuma taimakawa wajen sauya manyan layukan wutar lantarki da bututun ruwa.
Dangane da ci gaban aikin gadar sama ta Abakpa, injiniyan da ke kula da aikin, Injiniya Chimalo Ezeugo, ya bayyana cewa ana ci gaba da aikin tushe (piling), inda aka kammala guda 15 daga cikin guda 40 da ake buƙata.
Ya ƙara da cewa aikin, wanda tsawonsa ya kai kusan mita 800, ana sa ran kammala shi cikin shekara guda.
