ADC ba ta da abin ba wa ’yan Nijeriya — Shettima
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya shawarci ‘yan Nijeriya kada su goyi bayan jam’iyyar ADC, inda ya ce babu wani abu da za ta iya bayarwa.
Ya yi wannan magana ne a ranar Laraba a filin baje koli na Gusau da ke Jihar Zamfara, yayin da yake jawabi ga magoya bayan jam’iyyarsa.
Shettima ya ce ADC “ba komai ba ce,” inda ya kwatanta ta da ƙashin da ba shi da nama ko kaɗan.
“Shin kun san ADC? Ba ta da abin da za ta ba ku, don haka kada ku bi ta,” inji shi.
Ya ƙara da cewa jam’iyyar ba ta da abin da da ake buƙata domin jagorantar ƙasa ko kawo ci gaba ga ’yan Nijeriya.
Wannan kalamai nasa sun jawo hankalin jama’a a yayin da ake ci gaba da tunkarar babban zaɓen 2027.
A wani labarin kuma, tsofaffin gwamnonin Jihar Zamfara, Hon. Bello Mohammed Matawalle kuma ƙaramin ministan tsaro da Sanata Abdulaziz Yari sun amince Gwamna Dauda Lawal ya zamo ɗan takarar gwamna a shekarar 2027.
Sun yi wannan jawabin ne a lokacin bikin karɓar gwamnan zuwa jam’iyyar APC wanda mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shatima ya jagoranta a ranar Talata da ya gudana a Zamfara Trade fair compleɗ a Gusau.
Matawalle ya buƙaci magoya bayan sa da su goyawa Gwamna Dauda Lawal baya a zaɓen da ke tafe.
“Ina so in sanar da dukkanin magoya bayana cewar daga yau na aminta Gwamna Dauda Lawal shine ɗan takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar APC, kuma ina kira garesu da su goya masa baya a zaɓen dake tafe,” inji Matawalle.
Hakazalika, Sanata Abdulaziz Yari ya bayyana goyon bayansa ga Gwamna Dauda Lawal a matsayin ɗan takarar Gwamna a shekarar 2027.
Sanata Abdulaziz Yari ya ƙara da cewa jam’iyyar APC ta zamo abu ɗaya, yana mai nuni da cewar komawar Gwamna Dauda Lawal Jam’iyyar APC zai kawo haɗin kai da cigaban al’ummar Jihar Zamfara.
Ya yi kira ga mambobin Jam’iyyar APC da magoya bayan sa da su goyawa Gwamna Dauda Lawal baya a zaɓen dake tafe.Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ya yi kira ga mambobin Jam’iyyar APC da magoya bayan sa da su goyawa Gwamna Dauda Lawal baya a zaɓen dake tafe.