Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Nijeriya ta bayyana nadama tare da neman afuwar al’umma kan matsalolin katsewar wutar lantarki da ake fuskanta a sassa daban-daban na ƙasar, tare da jaddada cewa ana aiki tuƙuru domin kawo sauƙi cikin kwanaki masu zuwa.
Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin wani taron manema labarai da ya gabatar kan nasarorin da ma’aikatarsa ta samu cikin shekaru uku da suka gabata.
A cewarsa, matsalar wutar lantarki da ake fama da ita a halin yanzu ta janyo wahala ga jama’a, musamman a wannan lokacin rani da zafi ya tsananta a faɗin ƙasar.
“Na fito a hukumance ina ba da haƙuri ga ’yan Nijeriya bisa wannan matsala ta ɗan lokaci da ta jawo wahala, musamman a wannan lokaci na zafi. Lamarin ya shafi kasuwanci, makarantu da masana’antu baki ɗaya,” inji shi.
Ministan ya ƙara da cewa, duk da cewa gwamnati ba ta yi fatan shiga irin wannan hali ba, akwai wasu dalilai da suka wuce ikon ta, waɗanda suka haddasa matsalar.
Ya bayyana cewa babban dalilin matsalar shi ne ƙarancin iskar gas da ake bai wa kamfanonin samar da wutar lantarki, sakamakon tarin bashin da ake bin masu samar da iskar. Haka kuma, ya yi nuni da cewa rikicin da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya na iya ƙara ta’azzara matsalar idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba.
A Nijeriya, yawancin wutar lantarki ana samar da ita ne ta hanyar amfani da tashoshin da ke amfani da iskar gas. Sai dai rashin isasshen gas, matsalolin kula da bututun iskar, tsofaffin kayan aiki da kuma ƙarancin kuɗaɗe sun ci gaba da haifar da tangarɗa a ɓangaren.
Ministan ya bayyana cewa waɗannan matsaloli suna rage yawan wutar da ake iya samarwa, tare da ƙara yawan katsewar wuta da kuma rashin inganci a tsarin samar da lantarki.
Domin magance wannan ƙalubale, ya ba da shawarar a ƙara mai da hankali kan hanyoyin samar da makamashi na zamani, musamman na hasken rana da sauran hanyoyin da ba sa dogaro da babban grid na ƙasa.
A cewarsa, amfani da irin waɗannan hanyoyi zai taimaka wajen faɗaɗa samar da wuta cikin sauƙi da kuma rage nauyi a kan tsarin lantarki na ƙasa.
Haka kuma ya jaddada buƙatar haɗa makamashi daban-daban kamar na ruwa da hasken rana cikin tsarin lantarki domin ƙara ƙarfin samar da wuta da kuma rage dogaro da iskar gas kaɗai.
Ya ƙara da cewa, hakan na buƙatar zuba jari a tsarin sa ido da kula da grid domin tabbatar da cewa ana iya sarrafa sauye-sauyen makamashi yadda ya kamata tare da kiyaye daidaito.
Duk da haka, ministan bai bayyana matsayarsa ba kan ko zai tsaya takarar gwamnan Jihar Oyo a zaɓen 2027, duk da cewa ana raɗe-raɗin hakan a siyasa. Sai dai ya jaddada cewa burinsa shi ne ci gaba da yi wa ƙasa hidima a duk inda aka buƙace shi.
