
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Birgediya Janar Lawal Bature Mohammed (mai ritaya), wanda tsohon kwamandan rundunar Zamfara Community Protection Guards (CPG) ne, ya rasu bayan shafe watanni yana jinya sakamakon raunukan harbin bindiga da ya samu a wani hari da ‘yan bindiga suka kai wa jami’an tsaro.
Marigayin, wanda aka fi sani da Ɗan Gusau, ya samu munanan raunuka ne a wani kwanton-ɓauna da aka yi jami’an tsaro a bara, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Akan haka ne aka garzaya da shi zuwa ƙasar Misra domin samun kulawar likitoci na musamman, inda ya fara nuna alamun samun sauƙi kafin daga bisani rashin lafiyar tasa ta sake taɓarɓarewar har ta yi sanadiyyar mutuwarsa.
Sannan,tun a lokacin da yake jinya aka naɗa Muhammad Shehu Daligent a matsayin sabon kwamandan jami’an, matakin da ya zama wajibi domin tabbatar da ɗorewar ayyukan tsaro a jihar.
Wannan al’amari na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin jihar Zamfara ke ƙoƙarin karrama jami’an tsaro da suka rasa rayukansu.
Gwamnan Dauda Lawal na jihar ya jaddada aniyar gwamnatinsa ta tallafa wa iyalan jami’an da suka rasu a tare da karrama jarumtar da ‘yan CPG suka yi a bakin aiki.
Tuni dai aka yi jana’izar marigayin a unguwar Sabon Gari da ke Gusau a ranar Alhamis addinin Musulunci ya tanada.
