Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Hukumar jin daɗin Alhazzai ta jihar Kebbi ta kammala aikin samar da biza ga maniyyata aikin Hajjin bana.
Wannan sanarwar ta fito ne daga bakin Darakktan ICT Malam Faruku Jabbo a madadin Shugaban Hukumar Alhaji Faruku Aliyu (Enabo).
Ya bayyana cewa wannan hukumar ta yi wannan tanadin ne saboda ta sami isashshen lokaci don zuwa kasa mai tsarki wajen shirye-shiryen tanadin masaukan mahajjata a lokacin aikin Hajji na wannan shekarar ta 2026.
Ya yaba wa hukumar jin daɗin Alhazzai ta ƙasa bisa da sauran jami’an hukumar ta jihar Kebbi bisa ga jajircewar da suka nuna har aka samu nasarar kammala aikin cikin lokaci.
Haka-zalika ya yi kira ga maniyyata da su kasance jakadu nagari yayin zamansu a ƙasa mai tsarki, su guji aikata duk wani abu da zai iya zubar da kimar Nijeriya a idon duniya.
Ya kuma bayyana cewa hukumar a shirye ta ke da ta kare mutuncin maniyyata da kuma samar da buƙatun su a yayin aikin Hajji don ganin an yi aikin cikin natsuwa da kwanciyar hankali.
