Shugaban kamfanin Apple ya gargaɗi jama’a kan shagaltuwa da wayoyin hannu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban Kamfanin Apple, Tim Cook, ya bayyana damuwarsa kan yadda mutane ke amfani da wayoyin hannu, inda ya jaddada muhimmancin rage yawan kallon allon waya, wato screen, da kuma mayar da hankali kan mu’amala ta zahiri tsakanin jama’a.

Cook ya bayyana haka ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin talabijin na Good Morning America, inda ya yi gargaɗi kan illolin da ke tattare da yawan shagala da wayar hannu.

A cewarsa, bai kamata mutane su riƙa kallon wayoyinsu fiye da yadda suke kallon juna ido-da-ido ba, yana mai nuni da cewa mu’amalar zahiri ita ce ginshiƙin kyakkyawar rayuwa.

“Ba na son mutane su fi kallon wayoyinsu fiye da yadda suke kallon idanun juna,” inji shi.

Ya ƙara da cewa, duk da kasancewarsa shugaban ɗaya daga cikin manyan kamfanonin fasaha a duniya, har yanzu yana ganin cewa mu’amalar rayuwa ta zahiri ta fi muhimmanci fiye da hulɗar fasahar zamani.

Cook ya bayyana cewa, yawan yin “scroll” ba tare da iyaka ba ba hanya ce mai kyau ta ciyar da rana ba, yana mai shawartar mutane da su fita waje, su more yanayi, tare da gina dangantaka ta haƙiƙa da mutane.

Wannan furuci nasa ya janyo martani daban-daban daga masu amfani da shafukan sada zumunta, inda wasu suka amince da saƙon, yayin da wasu kuma suka nuna shakku, musamman ganin cewa kamfaninsa ne ke samar da irin waɗannan na’urori.

Wasu masu sharhi sun bayyana cewa kalaman Cook gargaɗi ne mai muhimmanci, wanda ya kamata a ɗauka da muhimmanci, yayin da wasu suka ce rayuwar yau ta tilasta mutane dogaro da wayoyi wajen aiki da nishaɗi.

Masana na ganin cewa wannan batu ya sake tayar da muhawara kan yadda fasaha ke tasiri ga zamantakewar al’umma, musamman yadda take rage kusanci da mu’amala ta zahiri tsakanin mutane.

A ƙarshe, Cook ya jaddada cewa daidaito shi ne mafita — amfani da fasaha cikin hikima ba tare da barin ta mamaye rayuwar ɗan Adam gaba ɗaya ba.

By ukarofi