Kano ta gaza yayin da jihohi 10 kacal ke fitar da cikakken rahoton kasafin ƙananan hukumomi – BudgIT

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wani sabon rahoto da ƙungiyar BudgIT ta fitar ya jefa Jihar Kano cikin zazzafar muhawara a faɗin ƙasa kan batun gaskiya da riƙon amana, bayan ya nuna cewa jihar na wallafa bayanan kasafin kuɗin ƙananan hukumomi ne ba cikakku ba, kuma wasu ma tsofaffi ne. Wannan lamari ya ƙara tayar da hankali kan yadda ake tafiyar da kuɗaɗen jama’a a matakin da ya fi kusa da talakawa.

Rahoton mai taken “Matakin da ya ɓace: Tantance Gaskiya da Buɗaɗɗen Kasafin Kuɗin ƙananan Hukumomi a Nijeriya” ya bayyana cewa akwai babban giɓi a tsarin bayyana gaskiya a harkar kuɗi a Nijeriya, musamman a matakin ƙananan hukumomi. Duk da cewa wasu jihohi na ƙoƙarin inganta tsarin, Kano da wasu jihohi sun kasa kai wa matakin da ake buƙata, inda suke bayar da bayanai kaɗan waɗanda ba sa nuna yadda ake rarraba kuɗi da kuma yadda ake kashe su.

A cewar rahoton, jihohi 10 kacal daga cikin 36 ne ke fitar da cikakkun bayanan kasafin kuɗin ƙananan hukumomi yadda ya kamata domin jama’a su fahimta. Waɗannan sun haɗa da Ekiti, Kuros Riba, Borno, Kaduna, Enugu, Kogi, Osun, Kebbi, Ebonyi da Yobe, kodayake har ma a cikinsu akwai bambanci wajen zurfi da ingancin bayanan da ake bayarwa.

Kano na daga cikin jihohi shida—tare da Imo, Ondo, Anambra da Ogun—da ke bayar da bayanai marasa cikawa ko kuma tsofaffi. Duk da cewa Kano na da wani dandali na duba binciken kuɗi (audit portal) tare da rahotannin aiki na kowane kwata, rahoton ya nuna cewa babu cikakken kasafin kuɗin shekara na ƙananan hukumomi, wanda hakan ke hana jama’a ganin cikakken hoton yadda ake tafiyar da kuɗaɗe.

A gefe guda kuma, rahoton ya nuna cewa jihohi 20 ba sa wallafa ko da ƙwayar bayanin kasafin kuɗin ƙananan hukumominsu. Daga cikinsu akwai manyan jihohi masu ƙarfin tattalin arziki kamar Legas, Ribas, Delta, Oyo, Edo da Akwa Ibom. Wannan, a cewar BudgIT, babban saɓani ne, ganin cewa yawancin waɗannan jihohi na wallafa kasafin kuɗinsu na jiha a yanar gizo, wanda ke nuna cewa akwai kayan aiki, amma babu cikakken niyya.

Rahoton ya jaddada cewa matsalar ba ta ƙarancin fasaha ba ce, illa dai rashin ƙudurin siyasa. A cewar ƙungiyar, idan aka ɓoye bayanan kasafin kuɗi a matakin ƙananan hukumomi, to ana katse damar jama’a wajen sa ido da tambayar shugabanni.

Duk da haka, rahoton ya nuna misalai na jihohin da suka yi fice wajen gaskiya. Ekiti ta yi zarra wajen wallafa cikakkun kasafin kuɗi na dukkan ƙananan hukumomi tare da sahihan takardu, yayin da Kuros Riba ke haɗa rahotannin bincike da bayanan ayyuka na lokaci-lokaci. Haka kuma, Borno na gabatar da haɗaɗɗun bayanai da tsare-tsaren inganta harkokin kuɗi.

Masana na ganin cewa buɗe kasafin kuɗin ƙananan hukumomi zai bai wa jama’a damar fahimtar manufofin gwamnati, bin diddigin yadda ake kashe kuɗi, da kuma riƙe shugabanni da alhaki. Amma a halin yanzu, yawancin waɗannan bayanai na ɓoye ne a takardu, ba tare da jama’a sun samu damar ganinsu ba.

Ga Jihar Kano, wannan rahoto ya sake jaddada buƙatar ƙara himma wajen tabbatar da cikakkiyar gaskiya a harkokin kuɗi, musamman a matakin ƙananan hukumomi. Masana na cewa lokaci ya yi da jihohi za su wuce matakin bayar da bayanai kaɗan, su rungumi cikakken tsarin buɗe bayanai domin ƙarfafa dimokuraɗiyya da amincewar jama’a.

A ƙarshe, rahoton ya nuna cewa ƙarfafa gaskiya a matakin ƙananan hukumomi na da matuƙar muhimmanci wajen inganta dimokuraɗiyya a Nijeriya, kuma hakan ba zai samu ba sai an samu cikakken sauyi a manufar siyasa da kuma ƙudurin shugabanni.

By ukarofi