
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rahotanni sun bayyana cewa tsohon gwamnan Jihar Kano kuma jagoran Kwankwasiyya, Rabi’u Musa Kwankwaso ya bar jam’iyyar NNPP hukumance.
Hakan na zuwa ne ƙasa da kwana ɗaya da ake sa ran zai koka ADC, wato a gobe Litinin.
Kwankwaso ya ɗauki wannan mataki ne yayin da ake ta muhawara kan sauya sheƙar da wasu ‘yan siyasa ke yi saboda rikice-rikicen cikin jam’iyya.
A sanarwar da ya fitar a yau Lahadi Kwankwaso ya bayyana godiyarsa ga jam’iyyar da jagorancinta bisa damar da ta ba shi na kasance jigo kuma jagora acikinta.
A shekarar 2023 ne tsohon ministan tsaron ya tsaya takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin inuwarta.
