‘Yan bindiga sun kai hari wata mashaya a Jos, an kashe wasu da dama

Spread the love

Daga HABU ƊAN SARKI a Jos

Gwamnatin Jihar Filato ta sanya dokar hana zirga-zirga na tsawon awoyi 48, domin shawo kan rikicin da ya ɓarke cikin daren Lahadi, biyo bayan wani mummunan hari da wasu mahara masu ɗauke da makamai suka kai kan wata mashaya dake wani yanki na Anguwar Rukuba da ake ce wa ‘Gari Ya Waye’, a cikin Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa.

Rahotanni daga waɗanda abin ya faru a idanunsu sun ce maharan sun shiga anguwar ne akan babura suna harbin kan mai uwa da wabi, yayin da suka kashe mutane da dama.

Ko da yake kawo lokacin rubuta wannan labari, babu wani jawabi a hukumance daga rundunar tsaro ta ƴansanda dake jihar, amma wasu rahotanni daga waɗanda abin ya faru a idanunsu, na bayyana cewa mutane kimanin takwas ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suke asibitoci don samun kulawar likitoci.

Wasu bidiyoyi da ake yaɗawa ta kafafen sada zumunta na nuna yadda aka yi wa mutane mummunan kisa da bindiga, har da alamun sara da adda. Yayin da ake nuna gawarwarki cikin jini, da kwasfon harsasai da suka watsu a titi da cikin shaguna.

An ji muryoyin matasa cikin fushi suna bayyana rashin jin daɗin su da faruwar wannan al’amari, yayin da wasu ke alwashin ɗaukar fansa. Wakilinmu ya ga wani bidiyo da ake nuna alamun yadda wasu matasan Kirista, waɗanda suka fi yawa cikin anguwar, suke kashe wani matashin Musulmi, tare da sa wa gawar wuta.

Anguwar Rukuba, na daga cikin anguwannin da suka yi ƙaurin suna da yawan tashe-tashen hankula, musamman a duk lokacin da aka samu wani yamutsi tsakanin musulmi da kirista a Jos. Yayin da ɗaukar ramuwar gayya ke ƙara ruruta rikicin dake faruwa a garin, da ya daɗe yana fuskantar rashin zaman lafiya.

Gwamnatin Jihar Filato ta bakin kwamishinan watsa labarai ta Jihar Joyce Ramnap ta ce an sanya dokar ne domin daƙile bazuwar rikicin zuwa sauran sassan garin Jos, tare da kira ga jama’a da su zauna a gidajensu, kuma a guji ɗaukar doka a hannu, da kaucewa yaɗa jita-jita.

By ukarofi