Rikicin Gabas ta Tsakiya: Fafaroma Leo ya buƙaci a haramta hare-haren sama

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Fafaroma Leo, shugaban Cocin Katolika na duniya, ya yi kakkausar suka kan hare-haren boma-bomai daga sama, yana mai cewa, irin waɗannan hare-hare ba su bambance tsakanin fararen hula da mayaƙa, don haka ya kamata a haramta su gabaɗaya.

Ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, yayin da yaƙin da ke tsakanin Amurka da Isra’ila da Iran ke shiga mako na huɗu a wani sabon jawabi da ya sake jaddada adawarsa kan yaƙi da tashin hankali.

Duk da cewa, bai ambaci wannan rikici kai tsaye ba a wani taro da ya yi da shugabanni da ma’aikatan kamfanin jiragen sama na Italiya, ITA Airways, Fafaroman ya nuna damuwa matuƙa kan yadda ake amfani da ƙarfin sojan sama wajen kai hare-hare a yaƙe-yaƙe.

A cewarsa, “Bai kamata wani mutum ya rayu cikin tsoron cewa, mutuwa ko halaka za su zo masa daga sama ba.”

Ya ƙara da cewa, darussan da duniya ta koya daga mummunan tarihin ƙarni na 20 ya kamata su zama hujjar hana irin waɗannan hare-hare gabaɗaya.

“Bayan irin bala’o’in da aka gani a ƙarni na ashirin, ya kamata a ce an haramta hare-haren sama har abada. Amma har yanzu ana ci gaba da su… wannan ba ci gaba ba ne, koma-baya ne,” inji shi.

Fafaroman, wanda shi ne na farko daga Amurka da ya jagoranci Cocin Katolika, ya sha yin kira da a tsagaita wuta a rikicin Iran, inda a ranar Lahadi ya bayyana yaƙin a matsayin “abin kunya ga ɗaukacin bil’adama.”

Kamfanin ITA Airways, wanda ke ƙarƙashin kamfanin jiragen sama na Jamus, Lufthansa, shi ne ke ɗaukar nauyin jigilar Fafaroma daga birnin Rome zuwa ƙasashen waje a lokutan tafiye-tafiyensa.

Masu lura da al’amuran duniya na ganin irin wannan kira daga babban jagoran addini na ƙara nuna damuwar da ake ciki kan tasirin yaƙe-yaƙe ga fararen hula, tare da ƙarfafa bukatar samun zaman lafiya a duniya.

By ukarofi