Yayata bidiyon ’yan ta’adda ma ta’addanci ne

Spread the love

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Haƙiƙa duk wani sabon faifan mugun rashin imani na ‘yan ta’adda kan fara bayyana ne a shafukan ‘yan bazata. Hakan tabbaci ne na hulɗarsu kai tsaye da miyagun na ƙurgurmin daji. Da zarar an fito da sabon faifai, za su yi wuf gaba ɗaya su yi ta yayatawa su na sharhi ba wai na hanyoyin magance ta’addanci ba, a’a sai hanyoyin ingiza jama’ar gari su ƙara shiga yanayin baƙin ciki. In wani ya yi caji ma da yawa har ya na ganin kamar ya fara yankar naman jikinsa ya cinye don ko zai ɗan huce takaici.

Duk lokacin da a ka ba da labarin samun maslaha ko zaman lafiya, ‘yan bazata na nan a baƙin ƙofa su na jira don su baƙanta hanyar da amfani da kalmomin la’ana da baƙaƙen maganganu da mummunar fata kamar zuriyar dujal don kar a samu nasarar da za ta kawo ƙarshen ƙalubalen. Abun da su ke son gani shi ne wani daga mafiya sharrinsu ya yi rubutu da zai kanbama hamayya da ƙiyayya ta ƙabilanci da muzanta aƙidar tauhidi ta hanyar sunaye daban-daban na neman a koma tsari na jahiliyya maimakon gyara da a ka samu na bin dokokin Allah da ya hana tsagerancin jajayen kunnuwa yin tasiri a Arewacin Nijeriya.

Sabbin faya-fayan ‘yan ta’adda na ɗauke da tsarin da duk wanda ke nazari in ya gani, zai fahimci tamkar ba su umurni a ke yi daga bayan fage na yanayin da za su dau faifan don ya zama silar tunzura jama’a su dau makamai su yi ta zubar da jinin juna ba tare da gano annamiman da su ka kyasta ashanar ba. Ni fa ina ganin akwai ma faya-fayan da sai an dauka fiye da sau ɗaya daratfa na cewa “A KAFTA”kafin mizanin ya gamsar da ‘yan bazata su fara yayatawa. Idan sun samu faifan da ya yi tsarin da su ke so irin na matashin nan mai yi wa ƙasa hidima NYSC, za su yi ta sarrafa shi ta yanayi daban-daban har sai sun kammala tsotse duk sharrin da ya ke ciki sun ga wasu masu hankali a cikin jama’a ma sun fada tafiyar don an rufta da su a makircin; ka ga mutum mai ilimi amma sai ya rubuta AREWA IS BLEEDING! Maimakon BANDITS WILL BE DEFEATED.

Bayan yayata faifan dan NYSC da cin kasuwar birni da kauye da faifan da tsara hotunan AI da sauransu, sai ga labarin ai matashin bai rasa ransa ba, Allah ya kiyaye shi daga mugun baki da mugun nufi, sai tsit ka ke ji ba mai son tada zancen. Yo tun da kun yayata faifan ta ko ina, ai nan ma tun da an samu labari mai dadi sai ku yi ta yayatawa har wadanda ku ka saka fashewa da kuka don takaici su yi ajiyar zuciya. Shin ko dai ku mugun labari ne kaɗai labari a wajenku? Kun zama dillalan sharri manzannin mutuwa.

Idan ka ga mutum ya maida aikinsa kullum gaggawar yayata bidiyon ‘yan ta’adda to tabbas ba ya son mugun yanayin ya kare ne kuma hakan shaida ce da cikin sauƙi a ke gane ɗan bazata. Shin wane shafi ne na miyagun irin nan kuma wa ke shiga shafukan ya ɗauko bidiyo in sun dora? Haƙiƙa mu dai a wajen ‘yan bazata mu ke ganin bidiyon ‘yan ta’adda don alamu na nuna su a ke Turawa su yayatawa duniya don zafafa Lardin Arewa da zummar tunzura jama’a su shiga dauki ba daɗi da juna ko ma su yi wa gwamnati tawaye.

Shin kun taɓa ganin bidiyon tare hanya da yanka matafiya a shafukan ‘yan bazata? Shin kun taɓa ganin suka ga Namdi Kanu ko ayyukan aware na ƙungiyarsa a shafukan bazata? Amma na tabbata kun ga yadda ‘yan bazata ke ba da kariya ga Zidane Kajuru duk da kotu ce ta same shi da jagorantar zugar da ta sheke fiye da mutum 66 da ba su yi ma sa laifin komai ba. Jinin waɗannan mutun 66 ya tafi a banza amma a wajen Bazatawa tun da kamar kwamandansu ne ya busa tabar wiwi kan wuyan miskinan.

Lokacin da ‘yan ta’adda su ka yi kisan gilla ga mai martaba Sarkin Gobir Alhaji Isa Muhammad Bawa na Gatawa, ɗan marigayin da a lokacin su ke tare ne ya ruwaito cewa ɗan majalisa Almustapha Boza Gobir ne ya ɗau nauyin mugun aikin wai da ladar naira miliyan 5. Akwai faifan bidiyon. Wallahi sai da mu ka yi tsayin daka wajen ƙaryata labarin kafin ƙurar ta lafa don sam ɗan ta’adda ba zai taba furta gaskiya ba, don haka daukar maganarsa da wani muhimmanci babban kuskure ne in ba a wajen ‘yan bazata ba.

Don haka da waɗannan miyagun na gabar da waɗannan na yamma da tsakiya duk ba wata ribar ribibin yayata bidiyon da su ke fitarwa matuƙar mutum ba abokin burminsu dillalin ‘yan bazata ba ne wadanda farin cikinsu a wayi gari Arewa kakaf ta kama da wuta balbal a doron yaƙin ƙabilanci don shafe ‘yan uwantakar Musulunci da samun ƙofar ƙarfafa bijirewa dokokin Allah da na kasa. ‘Yan bazata ba sa zaune a duk yankunan da fitinar nan ke aukuwa hasalima wasu na Nijar, Kamaru, Ghana da Sudan kuma alamu na nuna su na karɓar umurni daga tungarsu ta Midibelawa da dama ƙin jinin Hausawa da Arewa ya yi mu su kanta a zuciyarsu.

Ina labarin saukar jirage masu saukar angulu? Ina labarin masu safarar makamai da miyagun kwayoyi ga mutan na daji? Shin sai na cika shafi ne da bayanai kafin a gane? An yi walkiya.

In mun ce ajanda ce tafiyar ‘yan bazata sai ka ga masu shafukan bogi matsorata sun yi caa su na fesa gubar baƙar magana har da tsinuwa, la’ana da duk hanyoyin huce zafin jahilci, lalaci da rashin tarbiyya. Tabbas mutanen nan in ma su na da wata alaka da Hausawa ba ta wuce yadda su ka tsani Hausawa ba, don yadda Hausawa su ka rungumi addinin tauhidi, su kuma sun fi son ko a biyewa tsarin jan kunne ko mutane su yi ta sakarcinsu kawai a doron kasa daga duniya sai Kaduna.

Misali daya ne tak ma a nan na ke son magana a kai ba ma sai mun je 1903 inda kakannin ‘yan bazata su ka shiga rundunar jan kunne su ka sheƙe duk wani mai tauhidi da ya ɗaga mu su kara, amma jan kunne ya lura kakannin ‘yan bazata ba su da natsuwa ko limin jagoranci don haka ya bar jagoranci hannun sauran ragowar jama’ar Shehu. A nan ina son magana a kan kisan gillar kare dangi ga Hausawa a Zangon Kataf a 1992 da Atyap su ka yi. Marigayi Sarkin Zazzau Dallatu Uthman Yero a 1922 ya ware wani fili a yankin da ya ke Zangon Kataf na yau da a tarihi ya ke amsa sunan MABARADAU. A 1966 marigayi Sarkin Zazzau Malam Muhammad Aminu ya mikawa ‘yan kasuwa Hausawa su ka kafa kasuwa kuma don kasancewarsu Musulmi su ka kyamaci sayar da giya da naman alade a kasuwar. Wannan shi ne asalin musabbabin kwantaccen rikicin da ya kawo har ga kisan kare dangi na 1992 musamman na watan Mayu inda har mata masu juna biyu a ka farkewa ciki don tsananin mugunta.

Kar mu kai ga wani batun masu tare hanya a Gonin Gora ko rikicin Kajuru, Kasuwan Magani da sauransu da su Pastor James Moɓel Wuye da Sheikh Nuraini Ashafa ke ta wayar da mutane illar fitinar kiyayya. Shin a ina ne ko da layi ɗaya tak wani ɗan bazata ya taba kawo tarihin fitinar Zangon Kataf ya jajantawa Hausawa? In akwai mu na jira. Da gangan su ka tsallake 1992 su ka tafi har karni na 19 don murde wuyan tarihi. Shin wa ya taba ganin yadda ‘yan bazata kan murɗe wuyan kaza don ba su da ladubban yankawa cikin tausayi?. Idan su ka kawo shaidar bin bahasin Hausawa kan kisan gilla na Zangon Kataf zan yi saranda kuma na amince za a iya tattaunawa da su a fahimce su duk da a boye rufffff a wayar salula don sun san nakiyar da su ke bunnewa. 

KAMMALAWA

Har yanzu za mu iya gane ‘yan bazata ba sa kaunar koyarwar Shehu Mujaddadi ta ladubban rayuwar yau da kullum. Abu mafi sauƙi ma shi ne wajen yanka inda addinin ya koyar da idan mutum ya zo yanka dabba don samun naman miya da sauran buƙatu, to ya wasa wuka don kar ya wahalar da dabbar saboda ita ma kamar yadda mutum ke da rai, ita ma rai ne da ita. Saboda muguwaar zuciya, ‘yan bazata murɗe wuyan kaza su ke yi sai ta daina numfashi sai su wurga gawar a ruwan zafi. Haka su ke yi wa Akuya ta na wutsil-wutsil don sun murde kan sai ta saduda kafin su jefawa garwashin wuta. Watarana da na ga yadda su kan sheke kare sai da na kusan zubar da hawaye don gora su ke samu su dokawa tsakar kan karen, karen na ihu wui-wui amma ko a jikinsu haka za su yi ta maimaitawa har sai ya yi shiru sai su babbaka shi a kan guma-guman itatuwa ko su shiga aron aikin fawa.

Shehu ya koyar da yadda a ke tsarki bayan an biya buƙata a bayan gida da amfani da buta da ruwa ko in babu ga tsarin duwatsu, su ba sa son wannan sai mutum ya saita gabansa a kan titi ya cilla fitsarinsa ya na jika ma sa ƙafar wando bai dame shi ba, ya gama ya mayar ya ɗaure. Wasu matan bazata ma na gwada irin wannan ɗabi’a. Haka ma su kan sauke lodin bayan gida sai su shiga bahon ruwa su jika jikinsu da najasar kawai su fito wai ai sun yi tas da sabulu. Duk wannan don bijirewa Mujaddadi ne.

Haka ‘yan bazata su ke yi wa matafiya in sun tare su a hanya su make su ko su dau runtumemen dutse su tarwatsa kwanyar matafiyan don tsananin kiyayya ko su yi gutsil-gutsil da naman waɗanda su ka kashe don huce haushin da su ka gada na ba gaira ba dalili.

By ukarofi