Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin jihar Katsina ta ƙaddamar da wasu kwamitoci na musamman domin tsara yadda za a gudanar da shirin auren gata ga mata 1,000 tare da wayar da kan su kan muhimmancin zaman aure a musulunci.
Da yake ƙaddamarwar da kwamitocin, Kwamishinan ma’aikatan addini, Hon. Ishaq Shehu Dabai, ya ce shirin na da muhimmanci wajen rage matsalolin zamantakewa da kuma tallafa wa matasa da mata su samu ingantacciyar rayuwar aure, inda ya gode wa gwamnan jihar, Malam Dikko Umar Radda, bisa goyon bayan da ya bayar kan lamarin.
Shi ma Shugaban Hukumar Hizbah, Dr. Usman (Malam Abu Ammar), ya bayyana cewa, auren abu ne mai muhimmanci da tushe a addinin Musulunci tun daga zamanin Annabi Muhammad S.A.W, yana mai cewa shirin zai taimaka wajen ƙarfafa tarbiyya da zaman lafiya ga al’umma.
An raba kwamitocin zuwa yankuna uku ( Shiyyar Katsina, Shiyyar Funtua da kuma Shiyyar Daura) inda aka haɗa jami’an Gwamnati, Hisbah, Malamai da kuma mata domin tabbatar da nasarar shirin.
Haka kuma, taron ya samu halartar mutane daga ɓangarori daban-daban, yayin da mahalartan suka jaddada buƙatar haɗin kai domin ganin shirin ya yi nasara.
