YANZU-YANZU: Mutane sun mamaye farfajiyar INEC kan cire sunayen shugabannin ADC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

An jibge jami’an tsaro a farfajiyar Hedikwatar Hukumar Zaɓe (INEC) da ke Abuja sakamakon matakinta na soke kwamitin ayyukan (NWC) jam’iyyar ADC daga shafinta na yanar gizo.

Wannan al’amari ya janyo fargaba da yankin babban ofishin INEC da ke Maitama, inda aka ga sama da mutane 2,000 sun yi cincirindo suna gudanar da zanga-zangar lumana jim-kaɗan bayan sanar da ɗaukar matakin da hukumar ta yi.

An ruwaito cewa, da dama daga cikin masu zanga-zangar ‘yan ADC ne da kuma wasu ‘yan tafiyar Obidient Movement da wasu ƙungiyoyi da suka shirya gangamin da suka yi wa laƙabi da ‘Occupy INEC’.

A sanadiyyar haka ne aka toshe titin da ke kaiwa zuwa ga hedikwatar ta INEC da motocin jami’an tsaro yayin da aka dandazon jama’ar na tunkaro yankin.

Jami’an tsaron sun haɗa da na ‘yan sanda da hukumar tsaro ta farin kaya, DSS.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da INEC ta cire sunayen David Mark da Rauf Aregbesola a matsayin shugaba da sakataren jam’iyya a ADC daga shafin yanar gizon nata.

By Babaji