DSS sun kama wata matashiya mai kai wa ‘yan bindiga alburusai a Katsina

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Jami’an tsaron DSS sun kama wata matashiya mai suna Nafisa Usman mai shekaru 25 da alburusai na bindiga za ta kai wa ɓarayin daji.

An kama Nafisa a tashar mota na unguwa uku dake birnin Kano bayan an kawo mata harsashin daga garin Lafia na jihar Nasarawa, ita kuma za ta kai garin ƙanqara na Jihar Katsina.

Nafisa ta ce asalinta ‘yar garin ƙauyen Zango ce da ke ƙaramar hukumar Ƙanqara a jihar Katsina, kuma a yanzu ta shiga wata na huɗu kenan a wannan baƙar sana’a na safaran makamai zuwa ga ɓarayin daji.

A cewarta wani Soja ne yake kawo mata makaman, sannan wani ɗan kasuwa ne a Kano ya shigar da ita cikin wannan mummunan sana’a.

Nafisa ta amsa cewa an kai mata da harshin mai tarin yawa daga Lafiya, jihar Nassarawa inda ita kuma za ta kai shi ga ɓarayin daji da ke sace mutane a Ƙanqara don neman kuɗin fansa.

By ukarofi