YANZU-YANZU: An shiga fargaba a Abuja yayin da aka baza sojoji da tankunan yaƙi a hedikwatar INEC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Al’umma sun shiga fargaba a yayin da aka ga dakarun soji da ‘yan sanda sun karɓe iko da hedikwatar Hukumar Zaɓe (INEC) da ke Abuja a ranar Alhamis bayan barazanar gagarumar zanga-zanga daga mambobin jam’iyyar ADC.

An ga wasu bidiyoyi da hotuna da suka karaɗe kafafen sadarwa da ke nuna tarin jami’an sojoji a farfajiyar INEC tare da tankunan yaƙi da kuma ‘yan sanda cikin shirin ko ta-kwana.

Bayyanar cincirindon jami’an a hedikwatar hukumar na zuwa ne bayan da INEC ta ɗauki matakin soke Kwamitin Ayyukan (NWC) ADC daga shafinta na yanar gizo.

An ruwaito cewa sama da fusatattun ‘yan Nijeriya guda 2,000 ne suka yi gangamin a hedikwatar da ke yankin Maitama a Abuja jim-kaɗan bayan ɗaukar matakin.

Rahotanni sun bayyana cewa, dama daga cikin masu zanga-zangar ‘yan ADC ne da kuma wasu ‘yan tafiyar Obidient Movement da wasu ƙungiyoyi da suka shirya gangamin da suka yi wa laƙabi da ‘Occupy INEC’.

A sanadiyyar haka ne aka toshe titin da ke kaiwa zuwa ga hedikwatar ta INEC da motocin jami’an tsaro yayin da aka dandazon jama’ar na tunkaro yankin.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da INEC ta cire sunayen David Mark da Rauf Aregbesola a matsayin shugaba da sakataren jam’iyya a ADC daga shafin yanar gizon nata.

By Babaji