Trump ya sassauta takunkumin mai ga Cuba, ya buɗe ƙofa ga Rasha

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya nuna alamar sauya matsayinsa kan hana kai mai zuwa ƙasar Cuba, inda ya bayyana cewa ba shi da wata matsala idan kowace ƙasa ta aika da man fetur zuwa ƙasar, duk da kasancewar wani jirgin mai na Rasha ke daf da isa tashar jiragen ruwa na Cuba.

Rahotanni sun nuna cewa wani jirgin mai na Rasha da aka sanya wa takunkumi, wanda ke cikin abin da ake kira “jiragen inuwa” na ƙasar, yana bakin gabar gabashin Cuba, kuma ana sa ran zai isa tashar jirgin ruwa. Wannan jigilar mai na zuwa ne a daidai lokacin da tattalin arzikin Cuba ke fuskantar tsananin matsin lamba sakamakon katsewar hanyoyin samar da mai.

Tun farko dai, gwamnatin Amurka ta katse fitar da mai daga ɓenezuela zuwa Cuba bayan rikicin siyasa da ya shafi shugabanta Nicolas Maduro, lamarin da ya janyo ƙasashe da dama suka dakatar da aika mai zuwa Cuba, ciki har da Meɗico.

Shugaban Cuba, Miguel Diaz-Canel, ya bayyana cewa ƙasar ba ta karɓi wani jirgin mai ba cikin watanni uku, abin da ya ƙara tsananta matsalar makamashi da ta janyo katsewar wutar lantarki da kuma tsauraran matakan rarraba mai ga jama’a.

A yayin da yake magana da manema labarai a cikin jirgin Air Force One, Trump ya nuna damuwa kan halin da al’ummar Cuba ke ciki, yana mai cewa samar da makamashi na da muhimmanci ga rayuwar yau da kullum. Duk da haka, ya ci gaba da sukar gwamnatin Cuba, yana mai cewa tana da matsaloli na shugabanci da cin hanci.

Ya ce, “Idan wata ƙasa na son aika mai zuwa Cuba a yanzu, ba ni da wata matsala da hakan, ko Rasha ce ko wata ƙasa daban.”

Sai dai duk da wannan sassauci, Trump ya kuma bayyana cewa zai ƙara mayar da hankali kan Cuba nan gaba bayan kammala batun Iran, wanda ke cikin rikicin siyasa da tsaro a duniya.

A gefe guda kuma, rahotanni sun nuna cewa wannan jigilar mai daga Rasha na iya taimakawa Cuba na tsawon makonni uku zuwa wata guda kacal, bisa la’akari da yadda ake taƙaita amfani da mai a ƙasar.

Masana harkokin tsaro da tattalin arziki sun bayyana cewa hana wannan jirgin shiga Cuba na iya haddasa rikici tsakanin Amurka da Russia, musamman a wannan lokaci da ake fuskantar yanayi mai sarkakiya a siyasar duniya.

Bugu da ƙari, ana ganin muhimmancin Cuba ga Rasha na ƙaruwa, musamman bayan sauye-sauyen siyasa da suka faru a ƙasashe kamar Syria da ɓenezuela, da kuma matsin lamba da ake fuskanta a Iran.

A ƙarshe, wannan mataki na Trump na nuna sassauci na iya zama wata sabuwar hanya a dangantakar ƙasashen duniya, musamman dangane da yadda ake tafiyar da batutuwan makamashi da siyasa a matakin ƙasa da ƙasa.

By ukarofi