Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Asusun Lamunin Ilimi na ƙasa (NELFUND) ya bayyana cewa har yanzu alawus na kulawa da rayuwa da ake bai wa ɗalibai masu cin gajiyar shirin yana nan a kan Naira 20,000 a kowane wata, yana mai ƙaryata rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa an ƙara shi zuwa N25,000.
A cikin wata sanarwa da aka fitar a daren ranar Litinin, wadda Daraktar Sadarwa ta Tsare-tsare ta asusun, Oseyemi Oluwatuyi, ta sanya wa hannu, NELFUND ya gargaɗi ɗalibai da su yi watsi da duk wani bayani da ya saɓa da wannan, tare da jaddada cewa su dogara ne kawai da hanyoyin sadarwa na hukuma domin samun sahihan bayanai.
Sanarwar ta ce asusun ya lura da yaɗuwar bayanan ƙarya da suka shafi adadin alawus na wata-wata da ake bai wa ɗaliban da ke cin gajiyar shirin, lamarin da ya haifar da ruɗani a tsakanin masu anfani.
Domin kawar da wannan ruɗani, asusun ya bayyana a sarari cewa adadin alawus ɗin da aka amince da shi bai sauya ba, yana nan daram a N20,000 duk wata, sabanin yadda wasu ke yaɗawa cewa an ƙara shi.
NELFUND ya kuma buƙaci ɗalibai da su kasance masu lura da irin bayanan da suke karɓa daga kafafen sada zumunta, tare da gujewa yaɗa jita-jita da ka iya jefa mutane cikin ruɗani.
Hukumar ta ƙara da cewa, tana matuƙar godiya ga haɗin kan da ɗalibai ke ci gaba da ba ta, tare da jaddada aniyarta na ci gaba da gudanar da ayyukanta cikin gaskiya da inganci, domin tabbatar da cewa duk masu cin gajiyar shirin sun samu tallafin da ya dace a faɗin ƙasar nan.
A ƙarshe, NELFUND ta sake nanata ƙudurinta na tabbatar da gaskiya da riƙon amana a cikin dukkan ayyukanta, tana mai cewa za ta ci gaba da samar da bayanai na gaskiya domin amfanin ɗalibai da sauran jama’a.
