* Sun sake kira ga ‘yan sandan jihohi
Daga SANI AHMAD GIWA, Abuja
Gwamnonin jihohin Arewa 19 sun sake jaddada bukatar yin garambawul cikin harkar tsaro, ƙarfafa haɗin gwiwar yankin, da kuma zuba jari mai ɗorewa domin ci gaba.
A wani taro da suka gudanar a Abuja ƙarƙashin ƙungiyar Northern States Goɓernors’ Forum (NSGF), shugaban ƙungiyar kuma gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana cewa an samu “ingantaccen ci gaba” a harkar tsaro tun bayan taron da suka yi a watan Disambar 2025.
Sai dai ya gargaɗi cewa wannan ci gaba bai kamata ya sa a yi sakaci ba.
Da yake jawabi a wajen buɗe taron, Gwamna Yahaya ya ce dole ne yankin Arewa ya ƙara ƙaimi wajen haɗa kai domin tinkarar sabbin barazanar tsaro da ke tasowa.
Ya ƙara da cewa zaman lafiya da tsaro su ne ginshiƙin ci gaba, yana mai cewa babu wata gagarumar nasara da za a iya samu ba tare da kare rayuka da dukiyoyin jama’a ba.
Gwamnan ya bayyana cewa ɗaya daga cikin manyan matakan da aka cimma a taron baya shi ne ƙirƙirar Asusun Tallafawa Tsaro na Jihohin Arewa, inda ake sa ran kowace jiha za ta riƙa bayar da Naira biliyan 1 a kowane wata domin tallafa wa ayyukan tsaro a yankin.
Ya ce wasu jihohi sun riga sun fara cika wannan alkawari, ciki har da Nasarawa, Gombe, Borno, Kebbi da Kaduna.
Ya yaba wa waɗannan jihohi bisa matakin da suka ɗauka, yana mai kira ga sauran jihohin da ba su fara ba da su gaggauta fara bayar da gudummawar.
A cewarsa, nasarar wannan asusu za ta dogara ne da haɗin kai, jajircewa da kuma gaskiya wajen tafiyar da shi, inda ya ce kowace jiha za ta naɗa wakili domin kula da tsarin gudanarwa da sa ido.
Haka kuma, ya ce gwamnonin sun amince su bayar da Naira miliyan 500 kowannensu domin gina sakatariyar dindindin ta ƙungiyar NSGF, inda za a rarraba biyan kuɗin daga Disamba 2025 zuwa Afrilu 2026.
Ya ce jihohin Gombe, Nasarawa, Borno, Plateau, Zamfara, Sokoto da Kaduna sun riga sun fara biyan nasu kaso, yana mai fatan sauran jihohi za su bi sahu.
Baya ga batun kuɗaɗen tsaro, shugaban ƙungiyar ya ce suna kuma ƙoƙarin sake fasalin tsarin ƙungiyar domin ƙarfafa ayyukanta da inganta daidaita manufofi da tsare-tsare na dogon lokaci.
Ya ce wannan gyara na fara haifar da sakamako mai kyau, wanda zai taimaka wajen magance ƙalubalen yankin, musamman a fannin tsaro da kuma daidaita manufofi tsakanin jihohi.
Dangane da batun aikin ‘yan sanda, Gwamna Yahaya ya ce gwamnonin Arewa na ci gaba da goyon bayan kafa ‘yan sandan jihohi, yana mai cewa hakan ya zama wajibi bisa la’akari da halin rashin tsaro da ake ciki a ƙasar nan.
