An yi jana’izar ‘yan ƙauyen Benuwai 15 da aka halaka yayin da manoma ke biyan ‘yan bindiga tara

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Asabar aka gudanar da jana’izar mutane goma sha biyar da aka halaka a ranar 28 ga watan Yuli, 2026 a yankin Ƙaramar Hukumar Otukpo da ke Jihar Benuwai.

A cewar wani rahoto da AIT ya fitar, mazauna ƙauyen Efeyi-Utikpi ne suka jagoranci jana’izar, makonni bayan irin harin ya auku a ƙaramar hukumar.

Rahoton ya ce, harin ya yi sanadiyyar lalata gidaje da jefa al’ummar yankin cikin ƙunci da firgici, inda jagororin jama’a suke kira ga gwamnatocin tarayya da jiha su daina taƙaice matakinsu akan yin alla-wadai tare da ɗaukar matakan samar da cikakken tsaro da kariya ga ƙauyukan da ke fuskantar barazanar hare-haren ‘yan bindiga.

Wani wakilin ‘Equipping the Persecuted’, wato wata ƙungiyar Amurke mai zaman kanta, ya sanar da bayar da tallafi ga iyalan waɗanda suka rasu a sakamakon harin da kuma ƙungiyoyin ‘yan bijilante domin ƙarfafa musu wajen dawo da karsashinsu.

Wannan na zuwa ne ƙasa da makonni uku da wasu ‘yan bindiga suka kai wa al’umma farmaki a ƙauyen Otukpo-Nobi, inda aka kashe mutane takwas da aka gudanar da jana’izarsu a ranar 12 ga Yuli. A cewar rundunar ‘yan sandan jihar, manyan mutane biyar da yara uku ne harin ya yi sanadiyyar mutuwarsu.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Cletus Nwaduogbu ya bayyana al’amarin a matsayin harin ‘yan ta’adda da suka yi amfani da salon ‘guerrilla’ kafin tserewa zuwa bayan gari.

Waɗannan hare-hare na cigaba da sanya fargaba acikin manoma a jihar Benuwai kan halin tsaro a yankunansu, inda rashin tsaro ke hargitsa lamuran noma da ɗaiɗaita mutane daga mahaifarsu zuwa wasu wurare domin neman mafaka.

A wani labarin kuwa, wani manomi a yankin Gundumar Mbagena da ke Ƙaramar Hukumar Katsina-Ala ya bar zuwa gonarsa sakamakon wasu ‘yan bindiga sun buƙaci ya biya tarar Naira 500,000 kafin su bar shi ya nome abin da ya shuka.

By Babaji

Leave a Reply