EU ta musanta yin watsi da gayyatar INEC ta neman ta sanya ido a zaɓen 2027

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Litinin Jakadan Majalisar Tarayyar Turai (EU) ga Nijeriya da ECOWAS, Gautier Mignot a wata sanarwa, ya bayyana cewa, rahotannin da ke yawo cewa EU ta yi watsi da gayyatar da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta yi mata na neman ta sanya ido a babban zaɓen 2027 da ke tafe a Nijeriya ba gaskiya ba ne kuma jita-jita ce mara asali.

Mista Mignot ya tabbatar da cewa, majalisar ta sami saƙon gayyatar daga hukumar zaɓen Nijeriyar tun a watan Afrilu kuma ta bayar da amsa a kai, inda ta ce za ta tura ƙwararrun masana harkar zaɓe zuwa Nijeriya domin zaɓen waɗanda suka ƙunshi masu sanya ido masu zaman kansu mutum biyu zuwa huɗu.

Mignot ya ƙara da cewa, tawagar za ta tantance yadda ake gudanar da zaɓen bisa ƙa’idojin ƙasa da ƙasa, na yanki da na Najeriya, tare da gabatar da rahoto da shawarwari kan yadda za a inganta tsarin zaɓe a nan gaba.

Jakadan ya kuma bayyana cewa, zargin cewa EU ta ƙi sa ido kan zaɓen saboda taɓarɓarewar lamuran tsaro ko kuma abin da aka kira da “mu’amala mara kyau” bayan zaɓen shekarar 2023 ba su cikin wasiƙar da ta aike wa INEC, inda ya ce waɗannan hasashe ne da wasu ke yi kawai.

Haka kuma, EU ta ce tana yanke shawarar irin tawagar sanya idon da za ta tura zuwa ƙasashen da ke gayyatar ta ne bisa yanayin kowace ƙasa da kuma albarkatun da take da su, sannan tuni ta yanke shawarar gudanar da aikin tawagar ƙwararrun harkokin zaɓe a Nijeriya a zabn na 2027.

By Babaji

Leave a Reply