Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnatin tarayya ta ce ta ɗauki matakai domin rage dogaro da tallafin kuɗin da ake samu daga ƙasashen waje da ƙarfafa samar da kuɗi a cikin gida da ci gaba da mutunta abokan hulɗa na ƙasashen waje.
Muhammed Pate, ministan lafiya da walwalar jama’a, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a Abuja a wurin wani taron tattaunawa na lafiya da ƙasar Sin kan yadda za a shirya wa tunƙarar ɓarkewar annoba.
A yayin da yake duba kan irin ƙoƙarin daƙile cutattuka a duniya, Pate ya ce, duk da cewa tallafin ƙasashen waje ya taka muhimmiyar rawa wajen kawo ci gaba, sai dai annobar Kwabid-19 ta ɓullo da irin raunin tsarin lafiya da Nijeriya ke da shi da haɗarin dogaro da yawa da wasu.
“Ba zai yiwu ka ci da dogara tsarin kiwon lafiyarka wajen magance cutattuka kamar Maleriya da HIɓ da tarin TB ba a kan harajin da wasu ‘yan ƙasashe ba.”
“Haƙƙin kowacce gwamnati ce zuba hannun jari a fannin lafiya” ya faɗa.
Ya kuma ce Nijeriya ta za ta daina dogaro da kowanne irin tallafin ƙasashen waje daga nan zuwa shekara 2030 ta hanyar samar da kuɗi a hankali a cikin gida a mataki na gwamnatin tarayya da jihohi.
“Kashe kuɗinmu a kan tsari zai iya sawa mu cimma sakamakon da muke buƙata kamar yadda ake samju daga tallafin ƙasashen wajen.”
“Za mu iya samun zuba hannun jari da haɗin guiwa, sai dai haƙƙin samar da kuɗin ya rataya ne a wuyar gwamnatin Nijeriya,” ya faɗa.
Ya kuma nuna cewa za su ci gaba da haɗa kai da abokan haɗin guiwa na ƙasashen waje musamman waɗanda za su mutunta dokokin Nijeriya da tsare-tsare da makamantansu.
“Tsarin ɗaukar nauyin lafiya a duniya ya sauya a cikin shekarun 25 da suka gabata.”
“A yau, muna fatan samun ƙasa wacce za ta kasance jagaba wajen da ke zuba jari a fannin lafiya da hulɗa da duniya bisa yarjejeniya ta mutunta ƙasa da dokokinta,” inji Pate.
Ya kuma yi maraba da sabbin abokan hulɗa daga sauran ƙasashe da kamfanoni daga Amurka da Nahiyar Turai da Sin da sauransu, yana mai jaddada cewa lallai ne haɗa kai ta zama bisa doron mutuntawa da amfanin juna.
“Muna kan tafarkin samun ci gaba, kuma cigaban na zuwa da sauri.”
Haka kuma ministan ya bai wa George Gao – wanda ƙwararren masanin ƙwayoyin halitta ne ɗan ƙasar Sin – sarauta saboda irin gudunmowar da ya bayar a fannin lafiya.
A yayin da yake magana game da asalin sarautar a jihar Bauchi, ya ce wannan sarauta ta samo asali ne tun kafin kafa jihohin Nijeriya kuma ana bai wa mutane ne da suka ba wa al’umma gudunmowa.
“A matsayina na yaro daga karkara, na sa muhimmancin saraunta a ƙauyenmu. A yau, ina farin cikin ganin an karrama farfesa Gao da sarautar nan,” ya faɗa.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) ya rawaito cewa ƙasashe na samun tallafi a yayin da suke shiryawa ɓarkewar kowacce iriyar annoba domin inganta lafiya.
Sai dai da yawansu, zama cikin shiri abu ne mai muhimmanci inda masana ke cewa tattauna batun yadda za a zauna cikin shirin ɓarkewar cuta muhimmin abu ne wajen inganta tsarin lafiya.
