Tinubu ya naɗa Sanata Ida shugabancin Hukumar CAC

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da naɗin Sanata (Dr.) Ibrahim Ida a matsayin Shugaban Hukumar Rijistar Kamfanoni (CAC), tare da gabatar da sunayen wasu mutum bakwai domin cike guraben kwamishinoni a Hukumar ƙidayar Jama’a ta ƙasa.

A cikin wata sanarwa da Mai Ba Shugaban ƙasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai da Tsare-tsare, Bayo Onanuga, ya fitar, an bayyana cewa Dakta Ibrahim Ida ya kammala digirin digirgir (MSc) a fannin Banking da Kuɗi a Jami’ar Ibadan tun shekarar 1983, sannan ya samu digirin lauya (LLB) daga Jami’ar Abuja a 2003.

Kafin shigarsa Majalisar Dattawa a 2017 domin wakiltar Katsina ta Tsakiya, Ida ya riƙe muƙamin Kwamishinan Kuɗi na Jihar Katsina, sannan ya taɓa zama Babban Sakatare a ma’aikatar gwamnatin tarayya — muƙamai da suka ba shi gogewa mai zurfi a harkokin mulki da gudanarwa.

Haka kuma, Shugaban ƙasar ya miƙa sunayen wasu mutum bakwai domin zama Kwamishinonin Tarayya da za su wakilci jihohinsu a Hukumar ƙidayar Jama’a.

Waɗannan sun haɗa da Kolawole Oladipupo Alabi daga Ekiti, Nasiru Mu’azu daga Zamfara, Usman Abubakar Tuggar daga Bauchi, Dakta Isaka Alada Yahaya daga Kwara, Farfesa Sadiƙ Isah Radda daga Katsina, Suleiman Umar daga Jigawa, da kuma Honarabul Chiso Abdullahi Dattijo daga Sokoto.

An bayyana cewa waɗannan naɗe-naɗen za su fara aiki ne bayan samun amincewar Majalisar Dokoki ta ƙasa, kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

A wani ɓangare, Shugaba Tinubu ya kuma naɗa Dakta Yusuf Mohammed daga Kano a matsayin Shugaban Kwalejin Fasaha ta Tarayya da ke Kaltungo. Haka zalika, ya tabbatar da naɗin Bala Mohammed Bello a matsayin Mai Ba Shugaban ƙasa Shawara kan Tattalin Arzikin Siyasa.

Bello, wanda ya fito daga Jihar Kebbi, ya yi karatun Digiri a fannin Accounting da kuma MBA a Jami’ar Ahmadu Bello. Kafin wannan naɗi, ya taba zama Mataimakin Gwamna a CBN, sannan ya yi aiki a matsayin Daraktan gudanarwa a Nigerian Eɗport-Import Bank tsakanin 2017 zuwa 2022.

Shugaban ƙasar ya bayyana cikakken yaƙinin cewa dukkan waɗanda aka naɗa za su yi aiki tuƙuru wajen inganta manufofin gwamnatinsa, musamman wajen samar da ingantacciyar rayuwa ga ‘yan Nijeriya.

By ukarofi