Barayi sun sace cakulat mai nauyin tan 12

Spread the love

An sace tan 12 na cakulat ɗin KitKat, bayan da ɓarayi suka yi awon gaba da motar da ke ɗauke da su a da nufin raba su a sassan ƙasashen nahiyar Turai a makon da ya gabata.

Kamfanin Nestle da je ƙasar Switzerland ya bayyana cewa motar da aka sace tana ɗauke da sinƙi 413,793 na KitKat da ta ta tashi da su daga tsakiyar ƙasar Italiya domin rarraba su a sassan nahiyar Turai.

Kamfanin ya bayyana cewa motar ba ta kai ga inda aka nufa domin kammala rabon kayana a kasar Poland ba.

Har yanzu ba a gano inda motar ko kayan suke kaya ba, kuma kamfanin bai bayyana ainihin inda aka rasa su ba.

A wata sanarwa daban, KitKat ta ce ana iya gano sandunan da suka ɓace ta hanyar lambar batch code ɗinsu na musamman, inda duk wanda ya duba lambar zai samu umarnin yadda zai tuntubi kamfanin.

KitKat sun ce, “Ko da yake muna yaba wa zaɓin ɗanɗanon ɓarayin, abin da ya faru na nuna yadda satar kaya ke ƙaruwa a kasuwanci a kowane mataki.”

By ukarofi