Karin aure a wurin malam bahaushe

Spread the love

Daga AISHA ASAS

Mai karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin Iyali na jarida mai farin jini, Manhaja. Allah ya sa mu amfani juna, amin.

A yau darasin namu mai tsauri ne, don haka zan yi iya mai yuwa don ganin bai kasance rubutun da za a yi wa mummunar fahimta ba.

Kafin mu kai ga darasin namu, bari mu waiwayi abinda littafi mai tsarki Al’ƙur’ani ya faɗa game da auren mace fiye da ɗaya.

Allah mazaukakin Sarki Ya faɗa a cikin littafi mai tsarki, “Ku aura daga abinda ya yi muku daɗi na daga mataye, biyu, ko uku, ko huɗu, Idan kun ji tsoron yin adalci (a tsakanin matayen), to ku auri ɗaya.”

Na tuna wani ƙissa da aka ba mu da ta faru a zamanin Sarkin Musulmi Abubakar na III. An yi wani malami da da yake fatawar cewa, mata tara ne Allah ya halastawa Musulmi. Shi dai wannan malamin ya kafa hujja da kalmar ‘wa’ da ke nuni da ƙari, wato ‘da’ a matsayin dalilin da zai sa a haɗe adadin biyu da uku da huɗu.

Sarkin Musulmin ya ɗauki matakin da ya kamata kan malamin, wanda ba shi ne abinda muke son karkatawa kai ba, abinda nake son fitarwa, kalaman da suka biyo baya bayan da Sarkin ya nemi malamin ya janye furuncinsa ya ƙi, shi kuma ya yanke masa hukunci.

ɗaya daga cikin zan maimaita shin ko maza sun sana sanin sharuɗan da ya kamata su cika lafin su ƙara aurre?

Wannan dai ita ce maganar da malam bahaushe ya yi fatali da ita, wadda idan zai yi duba da ita, kuma ya yi wa kansa adalci, to da an samu gyara ga yawaitar saki da kuma ƙarin matsalolin da ke gudana a gidajen da ke ɗauke da mata fiye da ɗaya.

Da farko ya kai malam bahaushe, yayin da ka yi yunƙurin ƙara aure, wanda ya kasance babbar sunnah, ka yi duba zuwa ababe kamar haka;

1. Shin menene ƙarfin aljihunka?

Akwai wani adisi da yakee yawan yawo abakunan mutane, wanda wasu daga cikin malamai sun ce isnadinsa mai rauni ne, duk da cewa, ban yi dogon bincike kai ba, hadisin wanda aka ce wani bawan Allah ya je wurin ma’aikin Allah, ya sanar da shi talauci ya masa yawa, sai Manzon Rahma ya ba shi umurnin ya je ya ƙara aure.

A wannan suke cewa ƙarin aure, maganin talauci ne, don haka da sun ɗan sami wani abu da za su ciyar da iyalansu da ke cikin mawucin hali, sai ya tara shi ya ƙaro wata mata.

Idan muka ɗauki rayuwar wasu, za mu iya cewa, Allah bai kasance azallumin sarki ba, don haka ba za mu iya amincewa da cewa, ƙarin auren da za su yi na daga cikin umurnin ubangijin da suke iƙirari.

Mutumin da yake zaune da matar shi, da ‘ya’yanshi, ba abinda yake ba su, ko idan ya samo ma sai matar ta yi ‘yan dubaru, sannan za a ci, ba dai don an ƙoshi ba. ‘Ya’yanka na yawon gari, don samun ɗan abinda za su cike giɓin da iyayensa suka kasa cika masa.

Ba ka damu da inda suke zuwa ba, ko mai suke yi don su samu abinda suka ci ba, kawai dai ka zama silar zuwansu duniya, kuma tun a ɗaukar cikin nasu ne ka gama masu aikinsu. Duk wata hidima kan uwar yake. Ba ka ba su tarbiyya ba, wadda wajibi ce.

To da wannan ne za ka iya cewa ƙarin aure alheri ne gare ka?

Abu na biyu shi ne, lafiyar sauke haƙƙin aure. A nan ba wai ina magana kan iya lafiyar iya kusantar mace ba, har da halitta ta sha’awa.

Kamar yadda muka sani, a ɓangaren sha’awa ma Allah ya halicci mutane mabambanta, kamar yadda ya yi fari, baƙi, dogo da kuma guntu. Haka ma a ɓangaren sha’awa, akwai hariji, akwai mutawasiɗi, akwai kuma dakhili.

A ɓangangare na farko, shi ne namijin da mace ba ta isar sa, wanda a nasa ɓangaren ko mata nawa ne zai iya aura. Kuma ba a iya maza ne kawai ake samun wannan ɓangaren ba, har a mata, mun karkata ne da faɗin namiji domin darasin namu a nan ya karkata.

ɓanagare na biyu kuwa akwai matsakaici, shi dai ba hariji ba, kuma shi ba wanda ba shi da sha’awa ba. A wannan fagen an fi komai samun matsala, domin a irin waɗannan mutane za ka iya samun namijin da zai iya zama da mata huɗu kuma komai lafiya ba tare da ya tauye haƙƙin wata daga ciki ba. 

Haka kuma za ka iya samun wanda iya mace biyu ko ɗaya ce za a iya samun daidaito. To anan idan shi mai jikin bai iya yi wa kansa adalci ba, ko kuma bai fahimci kansa ba, zai iya jawo rigimar da ta fi ƙarfinsa.

Ma’ana dai shi ne zai iya faɗa wa kansa gaskiya mata nawa ne zai iya zama da su bisa adalci.

ɓangare na ƙarshe, shi ne wanda mace ba ta dame shi ba, kuma shi ba za a kira shi marar lafiya ba. Zai iya kusantar mace, amma idan zai yi shekara bai kusanceta ba ba shi da damuwa.

A wannan gaɓar zan so in yi misali da wata ƙara da aka taɓa kawo min ba da jimawa ba, wata mata ce mijinta ya ce zai ƙara aure, anan sai ta yi ta faɗa, a tunanin mutane kishi ne, amma lokacin da ta yi bayani sai na fahimci cewa, mijinta na daga cikin irin waɗannan maza kashi na uku, domin sai ta yi daƙyar yake kusantarta, don haka a lokacin da ya ɗauko zancen aure, sai ta tsammaci ita ɗin ce dai ba ya san kusanta, don haka ta yi iya mai yi don sanin ko wata matsala take da ita da ya sa ba ya kusantar ta, amma ya ce babu abinda yake tare da ita da ba ya so.

Ta bi abokane da neman shawara, sun aza ta kan neman maganin ni’ima, ba wani canji, ta je asibiti, an tabbatar mata ba ta tare da wani nakasu ko matsala da ka iya sa mijin ya gujeta.

Daga ƙarshe dai ta yanke shawarar kawai ta rabu da shi, inda ta ce ta dai fahimci sonta ne ba ya yi.

Da na yi magana da mijin ya tabbatar min da shi haka yanayin shi yake, da na tambaye shi ya yake tunanin zama da mata biyu alhali ko guda ɗayan dakyar ake tafiyar, a mamaki na sai ya sanar da ni ai yana da wadatar da zai iya auren mata har uku, ya iya ciyar da su da tufatar da su ba tare da sun rasa komai ba.

Wannan na ɗaya daga cikin kuskuren da maza ke yi, da yawa suna kallon ci da sha kawai ne ake buƙata a gidan aure, ba sa tunanin idan shi kaɗai ne, to mai zai hana macen ta yi zamanta a gidan babanta ya ci gaba da ciyar da ita.

Idan har ana so a samu zaman aure na kwanciyar hankali, to fa sai an cire son rai tun a lokacin da ake shirin yin auren. Shin zan iya riƙe mata biyu? Zan iya ba su ci da sha daidai gwargwado? Zan iya ba wa kowacce daga ciki haƙƙinta na aure ba tare da na tauye wata ba? Zan iya kula da abinda za a haifa min ba tare da na zube wa titi su ba da zummar almajiranci? Shin zan iya adalci a tsakanisu? Kamar yadda ayar da muka kawo ta ambata, wato “Idan kun ji tsoron kasa adalci a tsakaninsu, to ku auri ɗaya.”

Duk wani a abokanen ka da zai zuga ka wai kan cewa, nuna ƙaramta ne, kowa ya yi ƙari a abokanen ka, ko har na ƙasa da kai sun ƙara, don haka rashin ƙarin naka gazawa ce, kada ka bari waɗannan maganganu su yi tasiri gare ka ka ƙaro aure don su, domin duk arzikin ka, zai iya yiwa akwai abinda ba za ka iya cikawa ba daga cikin ababen da muka ambata, don haka kai ne kawai za ka iya yi wa kanka adalci yayin ƙarin aure.

Aure sunnah ce mai ƙarfi, haka ma ƙarin aure, don haka ba inda zai iya zama laifi idan ka nemi ƙara mata komai biyayya da kyautatawar da matarka ke yi maka, matuƙar dai za a bi yadda Allah ya ce a yi.

By ukarofi