2027: Babu damar tsaya wa takara ga ‘yan siyasar da suka haura shekaru 55 a ADC – Nafi’u

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaban tsagi na jam’iyyar ADC ya sanar da cewa jam’iyar ba za ta bar waɗanda shekarunsu ya haura 55 tsaya wa takara a ƙarƙashinta ba a babban zaɓen 2027 da ke tafe.

Da yake ganawa da BBC Hausa, kamar yadda Blueprint ta ɗauko, Nafi’u Bala ya bayyana cewa tsarin wanda ake shirin tabbatarwa na da nufin bai wa matasan ‘yan siyasa a Nijeriya damar faɗaɗa harkokinsu na jagoranci.

Ya kuma soki yadda ‘yan siyasar da shekarun su ja ke tururuwar shiga jam’iyyar, inda yake cewa yanzu lokaci ne da ya dace a bai wa ‘yan siyasar da ke da sauran ƙarfi da shekarunsu haura 55 ba dama.

A cewarsa, babban abin da suka sanya a gaba yanzu shi ne daidaita al’amuran jam’iyyar ta yadda za ta riƙa tafiya bisa tsariai kyau ga kowane ajin siyasa.

A kwanan nan jam’iyyar tana fuskantar matsalolin rikicin shugabanci, wanda ya kai ga tsagin hamayya na ƙoƙarin karɓe iko da lamuranta.

Wannan al’amari ya yi ƙamari ne a lokacin da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta ƙi amince wa tabbatar da kowane ɗaya daga cikin tsagin.

Kazalika, Nafi’u ya yi watsi da zargin cewa yana samun goyon bayan jam’iyya mai mulki APC domin nakasa ‘yan adawa yayin tunkarar babban zaɓen 2027, yana mai cewa wannan batu babu ƙamshin gaskiya acikinsa.

By Babaji