An yi jana’izar mahaifiin babban jami’in Blueprint a Ogun

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Al’umma da dama sun hallara yayin da aka yi jana’izar mahaifin Babban Daraktan Kudi da Asusu na Jaridar Blueprint a garin Ososa da ke Ƙaramar Hukumar Odogbolu ta Jihar Ogun.

Tun a ranar Juma’a ne aka fara hidimar domin karrama marigayin mai suna Pa Samson Idowu Oletubo, wanda ya rasu a ranar 13 ga watan Fabarairu bayan shafe shekaru 92 a duniya.

An ga yadda aka samu cinkoson ababen hawa ) a yankin da ba a saba gani duba da yadda ɗimbin jama’a suka halarci jana’izar.

Haka kuma gidan marigayin ya gaza ɗaukar adadin jama’ar da suka je domin yi masa bankwana bisa gagarumar hidimar da ya bai wa al’umma da yankin nasu.

Haka ma cocin da aka gudanar da addu’o’i, inda aka ga wasu mutane sun fake a waje.

By Babaji