Rahoton sirri ya bankaɗo shirin Boko Haram na kai hari filin jirgin Abuja da kurkukun Kuje

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wani rahoton sirri da ya fita daga cikin wata takarda ta cikin gida ya sake tayar da hankalin jama’a kan tsaron Babban Birnin Tarayya, Abuja, bayan da aka nuna yiwuwar mayaƙan Boko Haram na shirin kai hare-hare a wasu muhimman wurare.

Rahoton, wanda aka ce daga Hukumar Kwastom ta Nijeriya ya fito, kuma aka samu ta hannun jaridar News Point Nigeria, ya bayyana wasu muhimman wurare da ake zargin na iya zama maƙasudin hari.

Daga cikin wuraren akwai Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, da kuma wani gidan gyaran hali a cikin birnin.

Wata majiya mai tushe daga hedikwatar Kwastom, wadda ta nemi a sakaya sunanta, ta ce duk da cewa rahoton bai ambaci sunan gidan yarin kai tsaye ba, bayanan sirri sun nuna cewa ana zargin Gidan Yarin Kuje ne, inda ake tsare wasu da ake zargi da alaƙa da Boko Haram.

Majiyar ta ƙara da cewa, irin tsarin wannan barazana na nuna yiwuwar yunƙurin kuɓutar da waɗanda ake tsare da su tare da kai hare-hare kan wasu muhimman kadarorin ƙasa lokaci guda.

Rahoton ya kuma bayyana cewa jami’an tsaro na Nijeriya sun shiga shirin ko-ta-kwana sakamakon wannan bayani na sirri, domin daƙile duk wani yunƙuri na kai hari.

A cewar rahoton, wannan barazana na da kama da wani hari da aka kai a birnin Niamey na Jamhuriyar Nijar a watan Janairu, inda ‘yan ta’adda suka kai hari kan sansanin rundunar sojojin sama, lamarin da ya jikkata sojoji tare da lalata jirgin sama.

“Manufarsu ita ce kuɓutar da ‘yan ta’adda da ake tsare da su tare da haddasa mummunar ɓarna ga muhimman ababen more rayuwa na jiragen sama,” inji rahoton, yana mai nuni da alaƙa tsakanin wannan shiri da hare-haren da aka kai kan cibiyoyin jiragen sama a Nijar, musamman a Niamey da Tahoua.

Masana tsaro na ganin irin wannan tsari na iya nuna yunƙurin maimaita irin waɗannan hare-hare a cikin Nijeriya, lamarin da ke ƙara dagula yanayin tsaro.

Wannan lamari ya zo ne a daidai lokacin da ake ƙara nuna damuwa kan tsaro, bayan wata sanarwa daga Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka wadda ta bai wa wasu ma’aikatanta da iyalansu damar barin ofishinta da ke Abuja saboda yanayin tsaro.

Sai dai Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da wannan gargaɗi, tana mai cewa matakin kariya ne kawai bisa ƙa’idojin cikin gida, ba wai saboda wata barazana kai tsaye ba.

By ukarofi