Nijeriya ta yi gargaɗin yiwuwar samun ambaliya a jihohi 30

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayya ta fitar da rahoton hasashen ambaliya na shekarar 2026, inda ta yi gargaɗin cewa jihohi da dama ciki har da Legas, Bayelsa, Delta, Adamawa, Kebbi da wasu kusan jihohi 28 na iya fuskantar ambaliya mai tsanani yayin da damina ke gabatowa.

Ministan Albarkatun Ruwa da Tsabtace Muhalli, Injiniya Joseph Utseɓ, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin gabatar da rahoton a zauren liyafar Fadar Shugaban ƙasa da ke Abuja. 

Hukumar Kula da Ayyukan Ruwa da Yanayin Ruwa ta Nijeriya ce ta shirya taron, mai taken “Gudanar da Albarkatun Ruwa cikin Hikima: Sauyawa Daga Tattalin Arzikin Mai zuwa na Ruwa.”

A wajen taron, an samu wakilcin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta hannun Ministan Muhalli, da kuma Kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas, tare da jami’an gwamnati, shugabannin tsaro da abokan hulɗa na ci gaba.

Ministan ya jaddada cewa bayar da bayanai tun da wuri na taimakawa wajen ceton rayuka da dukiyoyi, tare da rage asarar tattalin arziki.

Ya bayyana cewa ma’aikatar na aiki kafaɗa da kafaɗa da Hukumar Kula da Yanayi domin inganta haɗin bayanan yanayi da ruwa, wanda ke da matuƙar muhimmanci ga manoma da masu tsara birane da kuma hukumomin kula da bala’o’i.

Rahoton ya nuna cewa ba wai binciken kimiyya kawai ba ne, illa kira ne ga ɗaukar matakan kariya kafin ambaliya ta auku. Duk da haka, ya gargaɗi cewa hasashe kaɗai ba zai wadatar ba matuƙar ba a ɗauki mataki a matakin al’umma ba.

Dangane da yankunan da ke cikin haɗari, rahoton ya nuna cewa sama da al’ummomi 14,000 a ƙananan hukumomi 266 cikin jihohi 33 da Abuja na cikin haɗarin ambaliya mai tsanani.

Haka kuma, an bayyana cewa fiye da al’ummomi 15,000 a ƙananan hukumomi 405 za su fuskanci matsakaicin haɗari, yayin da wasu yankuna za su fuskanci kaɗan.

Bugu da ƙari, an yi hasashen ambaliyar birane a manyan garuruwa kamar Abuja, Legas, Ibadan, Kano da Fatakwal sakamakon rashin ingantaccen tsarin magudanar ruwa. Haka kuma, jihohin gaɓar teku irin su Bayelsa, Delta, Legas da Ribas na iya fuskantar ambaliya sakamakon tashin ruwan teku.

Ministan ya yi kira ga gwamnatocin jihohi, hukumomin ƙananan hukumomi da shugabannin al’umma da su ɗauki wannan rahoto da muhimmanci, su kuma haɗa shi cikin tsarin gine-gine da tsara amfani da ƙasa. Ya jaddada cewa shiri tun da wuri shi ne hanya mafi inganci wajen rage illa.

A nasa jawabin, shugaban Nigeria Hydrological Serɓices Agency, Injiniya Umar Ibrahim Mohammed, ya bayyana cewa rahoton na 2026 ya samu ci gaba sosai, inda aka haɗa da sabbin fasahohi na zamani ciki har da amfani da na’urar AI domin inganta sahihancin hasashe da rage kuskure.

Haka kuma, ya ce hukumar ta inganta tsarin bayanai na ambaliya zuwa wani tsarin zamani da ke bada damar ganin halin da ake ciki kai tsaye, tare da ƙaddamar da manhajar wayar hannu domin sauƙaƙa samun bayanai ga jama’a.

Shi ma shugaban Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya, Farfesa Charles Anosike, ya nuna damuwa kan yadda ambaliya ke haddasa asara a Nijeriya da sauran ƙasashen Afirka, yana mai cewa amfani da fasaha wajen hasashe na taimakawa rage illar da bala’in ke haifarwa.

A ƙarshe, gwamnati ta jaddada cewa tsaron ruwa muhimmin bangare ne na tsaron ƙasa, tare da kira ga kowa da kowa ya haɗa kai wajen gina ƙasa mai juriya da kuma kare rayuka da dukiyoyi.

By ukarofi