Makarantar AKCILS za ta gudanar da taron cika Shekaru 50 a Kano

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Sashen hulɗa da tsofaffin ɗalibai na Kwalejin Aminu Kano ta nazarin addinin Musulunci da shari’a (AKCILS) da aka fi sani da (Legal) ya gudanar da wani muhimmin taro da wakilan azuzuwan tsofaffin ɗaliban kwalejin domin ci gaba da shirye-shiryen bikin cika shekaru 50 da kafuwar kwalejin.

An tsara gudanar da bikin na Golden Jubilee daga ranar 27 zuwa 29 ga Afrilu, 2026.

Taron ya bai wa mahalarta damar sanar da tsofaffin ɗaliban irin mataki da shirye-shiryen da aka kai, tare da karɓar shawarwari kan yadda za a tabbatar da cewa bikin ya gudana cikin nasara tare da haɗa kowa da kowa.

Mahalarta taron sun kuma tattauna hanyoyin ƙarfafa haɗin kai da daidaita ayyuka tsakanin ƙungiyoyin tsofaffin ɗalibai.

Bugu da ƙari, taron ya bai wa sashen damar sabunta bayanan ƙungiyoyin tsofaffin ɗalibai domin inganta sadarwa da kuma ƙarfafa dangantaka a tsakaninsu.

Daga nan sashen ya roƙi ƙungiyoyin tsofaffin ɗalibai da su ba da cikakken goyon baya ga ayyukan bikin ta hanyar halartar tarukan da kuma bayar da gudummawar kuɗi domin tabbatar da nasarar wannan babban biki na tarihi.

Da yake jawabi a wajen taron, daraktan hulɗa da tsofaffin ɗalibai, Malam Aminu Sadi Gabari, ya jaddada muhimmiyar rawar da tsofaffin ɗalibai ke takawa wajen ci gaban kwalejin, musamman a irin wannan muhimmin lokaci na bikin cika shekaru hamsin,

“Gudunmawar da muke buƙata a wajen ɗalibai guda biyu ce ta farko za’a iya ɗaukar wani aiki a makarantar a ɗauki nauyin yi ko kuma a taimaka wajen aiwatar da taron”.

Ya kuma yaba da irin huɓɓasa da wasu tsofaffin ɗaliban suka fara.

Shi ma mataimakin Provost mai kula da harkokin ilimi, Dr. Ali Tamasi Mu’az, wanda shi ne shugaban kwamitin shirya bikin, tare da mataimakinsa Dr. Umar Muhammad Kani, sun yaba da wannan yunƙuri tare da kira ga tsofaffin ɗalibai da su bayar da shawarwari, gudummawa da cikakken goyon baya domin ganin an gudanar da bikin cikin armashi da nasara.

Ya ce “Duk Nijeriya makarantar Legal ita ce ta farko da aka fara buɗe wa a Nijeriya ya zuwa yanzu akwai Legal guda 19 a ƙasar nan amma babu wacce ta kai ta Kano ci-gaba Allah mun gode maka” inji Dr. Tamasi

Taron ya jaddada ƙudirin kwalejin na ƙarfafa alaƙa da tsofaffin ɗalibanta a matsayin muhimman abokan hulɗa wajen ci gaba da ɗorewar martabar kwalejin da bunƙasar ta nan gaba.

By ukarofi