NAHCON ta gargaɗi jama’a kan ’yan damfara masu bizar bogi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Hukumar Alhazai ta Nijeriya, wato NAHCON, ta yi gargaɗi mai ƙarfi ga al’ummar ƙasar kan yawaitar ‘yan damfara da asusun sada zumunta na bogi da ke ikirarin samar da bizar aikin Hajji, duk da cewa hukumomin Saudiyya sun riga sun rufe bayar da bizar bana.

A cewar hukumar, Saudiyya ta rufe bayar da bizar Hajjin shekarar 2026 tun daga ranar 1 ga Shawwal 1447 Hijira (20 ga Maris, 2026), wanda hakan ke nufin an kammala duk wata sahihiyar hanya ta neman bizar aikin Hajji na bana.

Hukumar ta bayyana cewa an riga an tantance dukkan maniyyata da suka cancanta kafin wa’adin rufe bayar da bizar.

Ta kuma jaddada cewa ba a iya gudanar da aikin Hajji da kowace irin biza ba face ta Hajji kadai.

“Ba za a iya yin Hajji da bizar yawon bude ido, ta Umrah ko ta aiki ba. Bizar Hajji kadai ce ake amincewa da ita ta hanyoyin da suka dace,” inji sanarwar.

Hukumar ta kuma gargaɗi jama’a kan hukuncin da ke jiran duk wanda aka kama yana yin Hajji ba tare da sahihiyar biza ba, ciki har da ɗaurin watanni shida a gidan yari, tarar kuɗi har Riyal 20,000 (kimanin Naira miliyan 8.15), korar mutum daga kasar da kuma hana shi shiga Saudiyya na tsawon shekaru 10.

Ta buƙaci al’umma da su rika amfani da hanyoyin da aka amince da su kawai kamar tsarin Nusuk da kuma hukumomin jin dadin alhazai na jihohi, tare da kauce wa biyan kuɗi ga ‘yan damfara da ke alƙawarin samar da “tabbatacciyar biza.”

A ƙarshe, hukumar ta shawarci jama’a da su kasance masu lura tare da kai rahoton duk wanda ake zargi da damfara ga hukumomin tsaro domin ɗaukar matakin da ya dace.

By ukarofi