Gwamnatin Tarayya ta ƙulla yarjejeniyar dala biliyan ɗaya da kamfanin sarrafa ƙarafa na Indiya

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Gwamnatin Tarayya ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya (MoU) da wani babban kamfanin sarrafa ƙarafa na ƙasar Indiya mai suna Rashmi Metaliks Group, domin zuba jarin dalar Amurka biliyan daya (kimanin naira triliyan 1.5) a cikin shekara uku.

Ministan Raya Fannin Karfe, Prince Shuaibu Abubakar Audu, shi ne ya jagoranci tawagar Nijeriya zuwa birnin Kolkata na kasar Indiya, inda aka kulla wannan yarjejeniya bayan ya ziyarci masana’antar kamfanin.

Cikin wata sanarwa da Shugabar Sashin Yada Labarai na Ma’aikatar, Salamatu Jibaniya, ta fitar ranar Talata, Minista Audu ya bayyana matakin a matsayin gagarumin ci gaba da zai taimaka wajen farfado da fannin karfe a Nijeriya.

Ministan ya ce wannan jari zai bunkasa masana’antu a kasar nan, ya samar da ayyukan yi ga dimbin matasa, sannan ya rage dogaro da shigo da karafa daga kasashen waje, wanda hakan zai taimaka wajen adana kudaden kasashen waje.

Yayin rangadin da ya gudanar a masana’antar, Prince Audu ya jinjina wa yadda kamfanin ke amfani da fasahar zamani da kuma tsarin aiki mai inganci, inda ya ce hakan abin koyi ne ga Nijeriya wajen inganta harkar karfe.

Ministan ya kara da cewa Nijeriya na da burin daina zama kasar da ke fitar da danyen ma’adinai kawai, inda take kokarin komawa kasar da ke sarrafa su da kanta. Ya bayyana cewa Nijeriya na da sama da tan biliyan uku na danyen karfe (iron ore) masu inganci.

“Muna da danyen karfe mai ingancin kashi 67 cikin dari, kuma kudin da ake kashewa wajen sayen karfe a Nijeriya duk shekara ya kai dalar Amurka biliyan 10,” in ji shi.

Ya kara da cewa Nijeriya na da burin zama matattarar karfe a nahiyar Afirka, tare da shirin samar da tan miliyan 10 na danyen karfe duk shekara kafin zuwa shekarar 2030.

A nasa bangaren, Mataimakin Shugaban Kamfanin Rashmi Metaliks Group, Mista Sunil Patwari, ya yabawa kokarin Nijeriya na farfado da fannin karfe, inda ya bukaci gwamnati ta ba su dukkan goyon bayan da ya dace don tabbatar da nasarar ayyukan da ke kunshe a yarjejeniyar.

Rahotanni sun nuna cewa kafin Ministan ya dawo gida, zai gana da takwaransa na kasar Indiya, Shri Kumaraswamy, domin kara tattauna hanyoyin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannin hakar ma’adinai da kera karafa.

By ukarofi