
Gwamnatin Lebanon ta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra’ila ta kwanaki 10, domin samun damar tattaunawa don samar da cikakkiyar yarjejeniya ta dindindin.
A farkon makon nan wakilan gwamnatin Lebanon da Isra’ila suka halarci Washington domin tattaunawa ta kai tsaye, inda suka gana da Shugaban Amurka, Donald Trump a fadar White House.
Bayan ganawar, Trump ya sanar da tsagaita wutar tsakanin bangarorin biyu, wanda ya ce za ta fara aiki da ƙarfe 5 na Yamma (agogon Amurka), kuma za ta ɗauki kwanaki 10.
Saidai ƙungiyar Hezbollah ta ce ba ta cikin yarjejeniyar da aka cimma, kuma za ta cigaba da kai kai hare-hare a Isra’ila matuƙar ta cigaba da kai hari akan Iran.
Wannan mataki na zuwa ne yayin da ake ƙoƙarin rage tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya bayan ɓarkewar yaƙi tsakanin ƙasashe da dama.
