Yadda aka gudanar da bikin turaren wuta na shekara-shekara karo na farko a Kano

Spread the love

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano

An gudanar da bikin turaren wuta na shekara-shekara karo na farko a birnin Kano, wanda ya gudana a dakin taro na Meena Event Centre da ke kan titin Lodge, karkashin shirya kamfanin By Ray, a jagorancin shugabar kamfanin, Hajiya Rahanatu Aliyu.

Bikin, wanda ya dauki tsawon kwanaki biyu daga ranar Asabar zuwa Lahadi da ta gabata, ya samu halartar manyan baki daga sassa daban-daban na kasar nan, ciki har da sarakuna, attajirai da sauran al’umma.

Da take jawabi a wajen bude taron, Hajiya Rahanatu Aliyu ta bayyana cewa babban makasudin shirya bikin shi ne domin nuna wa al’ummar Arewa da kuma ‘yan kasuwa cewa yankin Arewa na da abubuwan alfahari da ake sarrafawa a cikin gida, wadanda za su iya fafatawa a matakin duniya.

Ta ce harkar turaren wuta na da matukar muhimmanci, kasancewar tana daga cikin tsoffin sana’o’in gargajiya da ake dadewa ana yi a Nijeriya, kuma tana taka rawa wajen bunkasa tattalin arziki, ganin yadda mutane da dama ke cin gajiyarta.

Haka kuma, ta yi kira ga matasa da su rungumi kananan sana’o’in gargajiya maimakon jiran aikin gwamnati, domin samun dogaro da kai.

Shugabar kamfanin ta kuma nuna godiyarta ga Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, bisa halartar bude taron, da kuma Magajin Garin Kano, Alhaji Muhammadu Nasiru Inuwa Wada, tare da sauran mahalarta, inda ta yi musu fatan alheri.

A nasa jawabin bayan bude taron, Sarkin Kano ya bayyana turaren wuta a matsayin abu mai muhimmanci da tarihi a rayuwar dan Adam, wanda ake amfani da shi a sassa daban-daban na duniya.

Ya ce ya ji dadi ganin yadda kamfanin ya zamanantar da turaren wuta, yana mai cewa a baya irin wadannan kayayyaki sai an shigo da su daga kasashen waje ko kuma a gan su a kasashen waje kawai.

Sarkin ya kuma yi kira ga sauran masu sana’ar da su kara himma wajen zamanantar da sana’o’insu, yana mai jaddada cewa masarautar Kano a shirye take ta ba da goyon baya da gudummawa ga masu sana’o’in gargajiya domin bunkasa su da samar da ayyukan yi a cikin al’umma.

Mahalarta taron sun bayyana jin dadinsu da wannan biki, inda suka yaba da yadda aka sauya turaren wuta zuwa na zamani kamar yadda ake gani a manyan kasashen duniya.

Sun kuma bukaci kamfanin da ya ci gaba da shirya irin wannan biki a nan gaba domin bai wa wadanda ba su samu damar halarta a wannan karo na farko ba damar cin gajiyar shirin.

By ukarofi