Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya bayyana shirin sayar da kaso 10 cikin 100 na babbar matatar fetur ɗinsa ta hanyar wani gagarumin tsarin sayar da hannun jari na farko (wato IPO) a nahiyar Afirka, wanda ake sa ran za a aiwatar da shi a shekarar 2026.
Dangote ya bayyana hakan ne yayin wani taro da Atlantic Council ta shirya a birnin Washington, D.C., inda ya ce wannan mataki zai taimaka wajen jawo jarin dogon lokaci da kuma bunƙasa kasuwar jari ta Afirka.
A cewarsa, matatar Dangote za ta riƙa biyan masu hannun jari ribarsu ne da dalar Amurka bayan kammala rajistar a kasuwar jari, kodayake bai bayyana cikakkun bayanan kuɗaɗen da ake sa ran samu daga sayar da hannun jarin ba.
Dangote ya ƙara da cewa kamfanin ya naɗa Stanbic IBTC Capital Ltd., ɓetiɓa Adɓisory Serɓices Ltd. da FirstCap Ltd. a matsayin masu ba da shawara kan wannan gagarumin shiri na IPO.
Ya bayyana cewa shirin sayar da hannun jarin ya yi daidai da burinsa na zuba kimanin dala biliyan 40 cikin shekaru biyar domin faɗaɗa harkokin kamfaninsa a fannin tace mai, samar da takin zamani da kuma haƙar ma’adinai a faɗin nahiyar Afirka.
Dangane da shirin faɗaɗa ayyuka, Dangote ya ce suna da niyyar ninka samar da taki har sau huɗu, ƙara ƙarfin tace mai, da kuma kafa masana’antun potash da phosphate a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, tare da ayyukan tace tagulla a ƙasar Zambia.
Matatar mai mai iya tace ganga dubu 650,000 a rana — wadda ita ce mafi girma a Afirka — ta kai cikakken ƙarfin aiki a baya-bayan nan, lamarin da ya zo daidai da tangardar samar da mai a duniya sakamakon rikice-rikicen Gabas ta Tsakiya, wanda ya kara buƙatar kayayyakin man fetur daga matatar.
Haka kuma, matatar ta fara taka muhimmiyar rawa wajen samar da man jiragen sama zuwa ƙasashen Turai, abin da ke ƙara ƙarfafa matsayin Nijeriya a kasuwar makamashi ta duniya.
A nasa ɓangaren, babban mataimakin shugaban sashen tace mai, sinadarai da kasuwar mai a kamfanin ba da shawara na Wood Mackenzie, Alan Gelder, ya bayyana matatar a matsayin mai matuƙar riba.
Ya ce, bayanai sun nuna cewa fitar da dizal ya karu zuwa ganga 79,500 a rana a watan Afrilu daga ganga 73,600 a watan Maris, yayin da fitar da fetur ya ragu zuwa ganga 50,100 a rana daga kusan ganga 102,400 a baya.
Rahotanni sun nuna cewa wannan shiri na Dangote na iya zama wani muhimmin mataki da zai ƙara jawo masu zuba jari daga cikin da wajen Afirka, tare da buɗe sabon babi a ci gaban masana’antar makamashi a nahiyar.
