Magoya bayan El-Rufai sun fashe da kuka bayan alƙali ya bada umarnin ci gaba da tsare shi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Babbar Kotun Jihar Kaduna ta yi watsi da buƙatar bayar da belin tsohon gwamnan jihar, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, a ci gaban shari’ar da gwamnatin jihar ke tuhumar sa da almundahanar biliyoyin kuɗaɗe da kuma amfani da muƙaminsa ta hanyar da ba ta dace ba, inda nan take magoya bayan tsohon gwamnan suka fashe da kuka bayan alƙalin da ke jagorantar shari’ar, Mai Shari’a Darius Khobo, ya ɗage shari’ar zuwa makon farko na watan Yunin 2026, domin fara sauraron ainihin shari’ar.

Alƙalin ya bayyana cewa, bayan sauraron muhawarar ɓangarorin biyu, inda ake sa ran za a ci gaba da shari’ar kullum a zaman na gaba, don kammala ta a cikin hanzari.

Yayin da yake magana da ’yan jarida jim kaɗan bayan zaman kotun, wanda aka hana ’yan jarida shiga cikin kotun, lauyan El-Rufai, Ubong Akpan (SAN), ya nuna rashin jin daɗinsa kan matakin kotun na ƙin bayar da beli tsohon gwamnan.

Ya ce, “Kotun cikin hikimarta ta yanke cewa saboda Nasir El-Rufai tsohon gwamna ne, hakan na nufin zai iya tsoma baki a bincike. Saboda haka ba shi da haƙƙin samun beli a cikin zargin almundahanar kuɗi. Muna godiya ga Mai Shari’a kan ilimin da ya nuna, amma cikin girmamawa ba mu yarda ba. Faƙat.”

Akpan ya ƙara da cewa, tawagar lauyoyin kare El-Rufai za su ƙalubalanci hukuncin ta hanyoyin shari’a da suka dace.

“An dage shari’ar zuwa makon farko na watan Yuni, kuma za a riƙa sauraron ta kullum domin duba duk abin da ke cikin kundin shari’ar,” in ji shi, yana mai zargin cewa shari’ar da ake yi wa tsohon gwamnan tana da nasaba da siyasa.

“Tun daga farko, duk abin da ya shafi wahalhalun Nasir El-Rufai yana da alaƙa da siyasa. Wannan kawai ɓangaren shari’a ne. Za mu fuskanci duk abin da ya zo,” in ji shi.

Dangane da takardun masu gabatar da ƙara, babban lauyan ya ce, “Takardunsu ba su ɗauke da siyasa a rubuce. Takardun shari’a ne. Don haka za mu mayar da martani gare su. Wannan shi ne abin da doka ta buƙata mu yi.”

Tun da farko, Akpan ya yi jawabi ga magoya bayan El-Rufai a harabar kotu, inda da dama daga cikinsu sun nuna damuwa sosai, wasu ma suna zubar da hawaye kan wannan lamari.

“Dukkanku kuna nuna hali kamar wani ya mutu. Babu wanda ya mutu. Wani lokaci abubuwa na iya faruwa  a rikici, amma kada ku ji tsoro. Ku tashi tsaye. Za mu ci gaba da wannan gwagwarmaya kuma za mu yi nasara,” in ji shi, yana kira gare su da su kwantar da hankalinsu.

Wakilinmu ya lura cewa da dama daga cikin magoya bayan sun nuna alamun damuwa bayan ɗage shari’ar.

Kimnain kwana 62 ke nan El-Rufai ke tsare a hannun hukuma, tun a ranar 18 ga watan Fabrairu, 2026, in banda kwana uku da aka sake shi bayan rasuwar mahaifiyarsa daga ranar 27 zuwa 31 ga watan Maris, 2026.

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) ce ta gurfanar da El-Rufai a gaban kotu bisa tuhume-tuhume guda tara da suka shafi zargin cin zarafin muƙami, zamba da sauran laifukan kuɗi.

Tuhume-tuhumen sun hada da zargin cewa ya sa gwamnatin jihar Kaduna ta fitar da kusan Naira biliyan 11 ga wata kungiya da ba a yi mata rijista ba domin aikin layin dogo na cikin gari wanda ba a aiwatar da shi ba.

Ana kuma zargin sa da amincewa da karɓar kusan Naira miliyan 289.8 a matsayin kuɗin sallama daga aiki fiye da adadin da doka ta tanada, da kuma karkatar da sama da Dala miliyan 1.08 daga rancen Bankin Duniya.

Sauran zarge-zargen sun haɗa da bayar da kwangilar kyamarar tsaro ta CCTɓ ta Naira biliyan 4.6 ba bisa ƙa’ida ba, cin badaƙalar filaye, da kuma yunƙurin lalata bincike.

El-Rufai ya musanta dukkan zarge-zargen.

By ukarofi