An gudanar da taron walimar addu’o’i na musamman a Legas

Spread the love

Daga DAUDA USMAN a Legas

A ranar Lahadin da ta gabata ne shugabannin ƙungiyar gudanar da harkokin kasuwancin citta da tafarnuwa a Legas, da ke kasuwar ƙasa da ƙasa wato Mile 12 International Market a birnin Ikko, ƙarƙashin jagorancin babban shugaban kasuwar gaba ɗaya, Alhaji Shehu Usman Jibirin Samfam, da shugaban ɓangaren kula da kawo cigaban kasuwancin citta da tafarnuwa a Legas, Alhaji Yusuf Dauda Kofa (Turakin Kofa), suka jagoranci gudanar da taron walimar addu’o’i na musamman.

An shirya wannan taro ne domin neman amincewar Allah Ubangiji Ya ci gaba da zaunar da jihar Legas cikin zaman lafiya, tare da sauran jihohin Arewacin Nijeriya baki ɗaya.

Taron ya samu halartar malamai, shugabannin ɓangarori daban-daban, da sauran al’ummar kasuwar Mile 12 International Market.

Haka zalika, taron ya gudana ne a harabar masallacin ɓangaren ‘yan kifi da kankana da ke kasuwar Mile 12. Sheikh Malam Ibrahim, na’ibin babban limamin masallacin Juma’a na ‘yan Izala Mile 12, da Sheikh Malam Abdulnasir Mile 12, da kuma Sheikh Gwani Malam Tasi’u na masallacin ‘yan shinkafa Mile 12, su ne suka jagoranci sauran malamai wajen gudanar da addu’o’in.

A yayin taron, an kuma gabatar da ɗaura aure tsakanin Alhaji Muhammadu Bello, ɗan kasuwar citta da tafarnuwa, da amaryarsa Malama Khadija Alhaji Lawan, ‘yar kasuwar kabeji, inda aka yi musu fatan alheri da addu’ar zaman lafiya a aurensu.

Tun farkon buɗe taron da addu’a, an bai wa ɗaya daga cikin waɗanda suka assasa taron, Alhaji Bala Kofa, ɗan kasuwar citta da tafarnuwa, wanda kuma yake ɗaya daga cikin iyayen ango, damar yin jawabi domin sanya albarka a cikin taron. Ya bayyana farin cikinsa ga dumbin al’ummar da suka halarta daga Kano, Ibadan, da kuma cikin garin Legas, tare da yi musu fatan komawa gidajensu lafiya.

Haka kuma, ya yi wa amarya da ango nasiha kan muhimmancin haɗin kai da zaman lafiya a rayuwar aure. Daga nan sai ya yi bayani kan irin cigaban da aka samu a kasuwancin citta da tafarnuwa a Legas, inda ya ce sun kwashe shekaru da dama suna gudanar da sana’ar, tun daga lokacin da ake sayen buhun tafarnuwa da citta kan naira ɗari uku, zuwa yanzu da ake sayensa tsakanin naira dubu ɗari huɗu da hamsin zuwa dubu ɗari biyar.

Ya ƙara da cewa babu abin da ya rage musu face su yi wa Allah godiya bisa ni’imar da Ya ba su na ci gaba da gudanar da sana’ar. A ƙarshe, ya jinjinawa shugaban ɓangaren kula da kawo ci gaban kasuwancin citta da tafarnuwa, Alhaji Yusuf Dauda Kofa (Turakin Kofa), bisa ƙoƙarin da yake yi wajen haɗa kan ‘yan kasuwa da bunƙasa harkar kasuwancin gaba ɗaya

By ukarofi