Netflix na ƙara zuba jari a Nollywood duk da ƙalubalen tattalin arziki 

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

Masana’antar fina-finan ta Kudancin Najeriya, wato Nollywood na ci gaba da samun karɓuwa a idon duniya, bayan da manyan kamfanonin watsa shirye-shirye suka ƙara nuna sha’awa wajen zuba jari a cikinta.

Rahotanni daga manyan kafafen labarai na ƙasa da ƙasa sun nuna cewa, kamfanin Netflix na cikin gaba-gaba wajen tallafa wa masana’antar, inda yake ƙara saka jari a sabbin fina-finai da shirye-shiryen talabijin na Najeriya.

A cikin ‘yan kwanakin nan, an sanar da wasu sabbin ayyuka da ke tafe, ciki har da:

Fina-finai masu dogaro da labaran Afirka, shirye-shiryen talabijin da za su kai ƙasashen duniya, da kuma haɗin gwiwa tsakanin ‘yan Najeriya da kamfanonin waje.

Wannan ya ƙara tabbatar da cewa Nollywood ba wai kawai ta cikin gida ba ce, har ma ta zama ɗaya daga cikin manyan masana’antu a duniya.

Duk da wannan cigaba, masana sun nuna cewa Nollywood na fuskantar ƙalubale masu yawa, ciki har da; hauhawar farashin kayayyakin aiki, ƙarancin kuɗaɗen samar da fina-finai masu inganci.

Wasu masu shirya fina-finai sun bayyana cewa, sauyin darajar kudancin Najeriya da hauhawar farashi na rage musu damar samar da manyan ayyuka.

Fitattun jarumai kamar Genevieve Nnaji da Richard Mofe-Damijo sun jaddada cewa lokaci ya yi da za a ƙara saka jari a cikin gida, tare da samar da tsare-tsare masu ɗorewa domin bunƙasa masana’antar.

Sun kuma bayyana cewa, haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da masu zaman kansu na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da ci gaba mai dorewa a masana’antar.

Masana na ganin cewa yawan masu kallon fina-finan Najeriya a duniya na karuwa sosai, musamman a yankunan Afirka, Turai da kuma Amurka.

Hakan na faruwa ne sakamakon sauƙin samun fina-finan ta hanyar intanet, ƙaruwar ingancin labarai da ɗaukar hoto, shigar manyan kamfanonin duniya ire-iren su Netflix.

Duk da ƙalubalen da ake fuskanta, Nollywood na kan turbar zama ɗaya daga cikin manyan masana’antun nishaɗi a duniya. 

By ukarofi