Daga UMAR GARBA a Katsina
Dan majalisar tarayya mai wakiltar Kankia, Kusada da Ingawa, Hon. Abubakar Yahaya Kusada ya rasa damar sake tsayawa takara bayan kwamitin sasanci na APC ya mayar da kujerar zuwa ƙaramar Hukumar Ingawa.
Hon. Abubakar Yahaya Kusada ne ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook bayan taron kwamitin sasancin fitar da ɗan takarar jam’iyyar APC a yankin.
Dan majalisar ya bayyana cewa kwamitin sasancin ƙarƙashin jagorancin Arc. Ahmed Musa ɗangiwa ne ya yanke hukuncin cire Kankia da Kusada daga takarar kujerar majalisar tarayyar.
Matakin ya bai wa ƙaramar hukumar Ingawa damar fitar da ɗan takarar APC domin kujerar a zaɓe mai zuwa.
Tuni al’umma suka fara bayyana ra’ayoyinsu kan matakin a kafafen sada zumunta.
