Daga MAHD MUSA MUHAMMAD
A ci gaba da shari’ar zargin juyin mulkin kan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Nijeriya a gaban Babban Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja, wani jami’in soja ya bayyana yadda masu bincike suka bankaɗo ainihin zargin shirin juyin mulki da nufin kifar da gwamnatin Tinubu tare da bayyana alaƙar raba kuɗi da tsare-tsaren da ake zargin masu hannu a ciki da su.
Shaidan, wanda ya ce yana aiki da ɓanngaren rundunar ’yan sandan soji, wato Nigerian Army Corps of Military Police (NACMP), ya bayar da shaida ne a shari’ar wani tsohon manjo janar da wasu mutum biyar, waɗanda ke fuskantar tuhume-tuhumen cin amanar ƙasa, ta’addanci, ɓoye bayanan tsaro da safarar kuɗi ba bisa ƙa’ida ba.
Jami’in, wanda aka ɓoye sunansa, inda aka kira shi da ‘AAA’, ya ce, yana cikin tawagar bincike da aka kafa bayan tsohon Hafsan Sojojin ƙasa, Janar Olufemi Oluyede, ya samu rahoton sirri na cewa, Kanar Mohammed Alhassan Ma’aji da wasu suna shirin kifar da gwamnatin dimokuraɗiyya.
A ƙarƙashin jagorancin Daraktan Gurfanar da ƙara na Tarayya, Rotimi Oyedepo, shaidan ya tabbatar da cewa ya san dukkan waɗanda ake tuhuma, inda ya ce an kama su ne bisa zargin hannu a cikin shirin juyin mulkin da ya haɗa da sojoji da fararen hula.
Ya bayyana cewa bayan karɓar rahoton sirrin, an tantance shi kuma aka tabbatar da sahihancinsa, lamarin da ya sa aka ba su umarnin fara bincike.
A cewarsa, sun kama Kanar Ma’aji, sun kwato wayarsa ta Samsung Galaɗy, tare da gudanar da bincike a gidansa inda suka samu littafin rubutu da wasu muhimman takardu.
Ya ce littafin ya ƙunshi tsare-tsaren aiki, sunayen manyan jami’an gwamnati da aka tsara za a kai wa hari, har da waɗanda za a kashe idan shirin ya tabbata.
“Mun kuma samu bayanai kan sauye-sauyen siyasa da tsarin gwamnati da za a aiwatar bayan juyin mulki,” inji shi.
Binciken fasaha da aka yi wa wayar Kanar ya kuma bankaɗo cikakken tsarin shirin da kuma alaƙa tsakanin sa, wasu jami’an soja da waɗanda ake tuhuma a kotu.
Shaidan ya kuma bayyana cewa an gano hanyoyin kuɗi tsakanin Kanar Ma’aji, tsohon gwamnan Jihar Bayelsa, Timipre Sylɓa, da wasu daga cikin waɗanda ake tuhuma.
“Mun gano wasu kalmomin sirri da masu shirin ke amfani da su, tare da biyan kuɗaɗe ga wasu domin aiwatar da shirin,” inji shi.
Ya ƙara da cewa bincike ya gano wani kamfani mai suna Purple Waɓe wanda ake zargin an yi amfani da shi wajen samar da kuɗin shirin, inda EFCC ta bayar da bayanan mu’amalar kuɗin.
A cewarsa, an gano jerin kuɗaɗe da aka cire daga asusun kamfanin a ranaku daban-daban na watan Satumba zuwa Oktoba 2025, waɗanda suka kai miliyoyin naira, kuma bincike ya nuna cewa an karkatar da su domin tallafa wa shirin juyin mulki.
Ya kuma ce an gudanar da taruka a wurare irin su Green Land Apartment da Brookɓille Hotel a Abuja, inda ake tattauna yadda za a kifar da gwamnati tare da tsara waɗanda za a kai wa hari.
“Sun tsara yadda za su mamaye manyan hanyoyi da sansanonin soja, ciki har da barikin Neja, tare da raba muƙamai a tsakanin su bayan nasara,” inji shi.
Kotun, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Joyce Abdulmalik, ta amince da gabatar da wasu hujjoji ciki har da takardun otel da bayanan da aka samo daga wayar Kanar Ma’aji.
Haka kuma kotun ta ba da umarnin ɓoye bayanan shaidu bisa tanadin dokar Administration of Criminal Justice Act (ACJA) 2015, saboda tsaron su, duk da cewa lauyoyin waɗanda ake tuhuma sun nuna damuwa kan hakan. An kuma dage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 4 da 5 ga watan Mayu.
Gwamnatin Tarayya ta tuhumi waɗanda ake zargin da haɗa baki domin tayar da yaƙi kan ƙasa, laifin da doka ta tanada hukunci mai tsauri, tare da zarginsu da sanin shirin amma suka ƙi sanar da hukumomi.
Sai dai dukkan waɗanda ake tuhuma sun musanta laifukan, kuma a halin yanzu suna tsare a hannun Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) har zuwa lokacin da za a kammala shari’ar.
