Gwamnatin Kano za ta aurar da zawarawa da ’yan mata 3,000 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta sanar da shirin gudanar da wani gagarumin bikin aurar da zawarawa da ’yan mata dubu uku (3,000), wanda ya haɗa da maza 1,500 da mata 1,500.

Sheikh Aminu Daurawa, shugaban hukumar Hisbah ta jihar Kano ne ya bayyana hakan a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Laraba.

Shirin, wanda aka sanya wa suna “Auran Gata”, an ce ya fi mayar da hankali ne kan marayu da kuma ’ya’yan talakawa domin tallafa musu su samu ingantacciyar rayuwa ta hanyar aure.

A cewar bayanin Kwamandan na Hisbah, gwamnati ta tanadi kayayyaki da tallafi iri-iri ga sabbin ma’auratan. Daga cikin abubuwan da za a bayar akwai kayan ɗaki kamar gado, sif, madubi, katifa, filo da zanin gado, da kuma kayan abinci da suka haɗa da shinkafa, taliya da man girki.

Haka kuma, an tanadi kayan sawa ga mata da maza, inda mata za su samu atamfa da hijabi, yayin da maza za su samu shadda da hula.

Bugu da ƙari, kowace amarya za ta samu sadaki na Naira dubu ɗari (₦100,000), tare da ƙarin jari na Naira dubu ɗari (N100,000) domin fara sana’a.

Gwamnatin ta kuma bayyana cewa za a gudanar da gwajin lafiya ga dukkan waɗanda za su ci gajiyar shirin, tare da cike wasu takardu guda uku domin tabbatar da cewa sun cika sharuddan shiga.

Sai dai an jaddada cewa duk wanda zai shiga wannan shiri dole ne ya kasance yana da wata sana’a.

By ukarofi