Gwamna Dikko Raɗɗa ya jaddada muhimmancin adana tarihin Katsina 

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina 

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwar jama’a wajen rubutawa da adana tarihin jihar, al’adu da gadon gargajiya domin amfanin al’umma a gaba da kuma duniya baki ɗaya.

Ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi kwamitin da ya wallafa littafin “Katsina: A Tapestry of Time and Prospects” a ofishinsa.

Ya yaba musu bisa ƙoƙarin da suka yi wajen samar da littafi mai inganci, yana mai cewa ya dace ‘yan jihar su riƙa bayar da labarinsu da kansu maimakon a bar wasu su yi.

Gwamnan ya nuna damuwa kan yadda ake watsi da al’adu da wuraren tarihi, yana kira ga jama’a da su riƙa alfahari da asalin su. Ya ce littafin zai taimaka wa matasa su fahimci tarihinsu, sannan zai taimaka wajen inganta martabar jihar a idon duniya da kuma jawo masu zuba jari.

Sakataren Gwamnatin Jihar, Abdullahi Garba Fasakari, ya bayyana aikin a matsayin babbar nasara wajen tattara tarihin da al’adun Katsina.

Shugaban kwamitin, Farfesa Sani Abubakar Lugga, ya ce sun samar da sabon littafi mai inganci wanda ya kunshi tarihin Katsina tun daga zamanin da har zuwa yau, tare da bincike mai zurfi da hotuna na asali.

Kwamitin ya kuma ba da shawarar gyaran wuraren tarihi da kuma samar da shirin fim (documentary) domin ƙara bayyana tarihin jihar.

Gwamnan ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafawa duk wani shiri da zai bunƙasa ci gaban jihar da kuma kare al’adunta.

By ukarofi