Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa yaƙin da Amurka da Isra’ila ke yi da Iran na iya tunkuɗa sama da mutane miliyan 30 cikin talauci a duniya.
Shugaban shirin ci gaban majalisar (UNDP), Alexander De Croo ne ya bayyana hakan a gefen taron ƙasashen G7 a Paris, inda ya bayyana damuwa kan yadda rikicin ya jawo tashin farashin makamashi da takin zamani.
A cewarsa, “Wannan tamkar koma baya ne ga ci gaba. An ɗauki shekaru da dama ana gina tattalin arziki mai ƙarfi, amma cikin ‘yan makonni kaɗan yaƙi ya rusa shi.”
De Croo ya ce, binciken da suka gudanar ya nuna cewa ko da yaƙin ya tsaya a makonni shida kacal, mutane miliyan 32 a ƙasashe 160 za su shiga mawuyacin hali.
MDD ta ce ƙasashen Afirka ta Kudu da Sahara da wasu a Asiya za su fi shan raɗaɗi, sakamakon tsadar makamashi da ƙarancin taki, wanda ka iya shafar noma da rayuwar al’umma.
Haka kuma, an yi gargaɗin cewa rikicin na iya haifar da rashin kwanciyar hankali a siyasa da kuma raguwar kuɗaɗen da ‘yan ƙasashen waje ke turawa gida.
UNDP ta ce muddin ana son rage tasirin matsalar, ana buƙatar kusan dala biliyan 6 domin tallafa wa masu rauni, yayin da ake ci gaba da tattaunawa da Asusun Ba da Lamuni na Duniya IMF da kuma Bankin Duniya kan matakan ɗauka.
Yaƙin Iran ya janyo rufe Mashigar Hormuz, wadda aka yi ƙididdiga ita ce hanyar ruwa mafi muhimmanci a fannin tattalin arzikin duniya.
