Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta biya jimillar Naira biliyan 45.89 domin biyan basussukan giratuti da alawus-alawus ga ma’aikata 14,560 da suka yi ritaya a faɗin jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin bikin ranar ma’aikata ta shekarar 2026 da aka gudanar a filin wasa na Muhammadu Dikko da ke Katsina, inda ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na inganta jin daɗin ma’aikata.
Ya ce wannan biyan kudi wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnati na cika alƙawurran da ta ɗauka na kula da waɗanda suka yi wa jihar hidima tsawon shekaru.
Dangane da batun albashi, Malam Raɗɗa ya tabbatar da cewa gwamnatinsa na biyan ma’aikata albashinsu a kan lokaci, yana mai cewa duk ma’aikacin gwamnati a jihar na karbar albashinsa kafin ko a ranar 25 ga kowane wata.
Haka kuma, gwamnan ya sanar da ƙarin albashi da alawus ga ma’aikatan lafiya, ciki har da sabon tsarin albashi ga likitoci da kuma karin alawus na haɗari, domin inganta ayyukan kiwon lafiya a jihar.
A ɓangaren ɗaukar aiki, gwamnan ya ce an ɗauki sabbin ma’aikata a fannoni daban-daban, ciki har da ma’aikatan lafiya sama da dubu ɗaya, da kuma wasu ɗaruruwan ma’aikata a asibitoci da sauran hukumomi.
Bugu da ƙari, ya ce sama da ma’aikata 3,800 sun samu ƙarin girma a shekarar 2025, yana mai cewa hakan na daga cikin manufofin gwamnatinsa na ƙarfafa gwiwar ma’aikata.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa na karrama ma’aikata ƙwarai ta hanyar ba su kyaututtuka kamar motoci da kudade, tare da horas da dubban ma’aikata domin kara musu ƙwarewa.
A ɓangaren noma kuwa, ya ce an samar da taraktoci 400 da kayan tallafi ga manoma, tare da amfani da famfunan ruwa masu amfani da hasken rana domin bunƙasa noman rani.
Haka zalika, gwamnan ya ce an ɗauki malamai sama da dubu biyu tare da gina sabbin makarantu na zamani, da kuma ɓullo da shirin tallafawa mata ‘yan kasuwa sama da dubu 14 a jihar.
A ɓangaren matasa, gwamnan ya bayyana cewa an raba sama da Naira miliyan 252 ga matasa domin bunƙasa sana’o’insu, tare da ƙudirin faɗaɗa shirin a nan gaba.
Da yake nasa jawabin, Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta jihar, Dakta Hussaini Hamisu Yanduna, ya yaba da ƙoƙarin gwamnan, musamman wajen biyan basussukan gratuity da kuma aiwatar da mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000.
Sai dai ya buƙaci gwamnati da ta kara himma wajen samar da tsaro a wuraren aiki da hanyoyin sufuri, da kuma ɗaukar matakan rage raɗadin hauhawar farashin kayayyaki ga ma’aikata.
Bikin ya samu halartar manyan jami’an gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki a jihar.
