Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe
Wani gagarumin goyon baya na ƙara ƙarfi ga Zakariya Jidda yayin da mambobin ƙungiyar APC Youth Solidarity Group a Jihar Gombe suka fito fili suna marawa yiwuwar tsayawarsa takarar kujerar Majalisar Wakilai baya gabanin zaɓen 2027.
Wannan goyon baya na zuwa ne bayan shirin Jidda ma daukar nauyin tura matasa 30 daga ƙananan hukumomin Gombe, Kwami da Funakaye zuwa ƙasar China domin karatu, wani mataki da ake kallonsa a matsayin zuba jari mai muhimmanci wajen bunƙasa ilimin matasa da inganta rayuwarsu.
A wani taron tattaunawa da aka gudanar a Funakaye, hedikwatar ƙaramar hukumar Bajoga, ƙungiyar matasan tare da shugabannin al’umma da jiga-jigan jam’iyya sun yabawa wannan shiri, suna mai bayyana shi a matsayin alamar shugabanci nagari da kuma kishin cigaban al’umma.
Shugaban ƙungiyar, Kwamared Nura Shuaibu Musa, ya ce shirin tallafin karatun ya nuna adalci da haɗin kai, yana mai cewa an zaɓi waɗanda suka amfana daga dukkan ƙananan hukumomin uku cikin tsari mai kyau.
“Wannan shiri ya wuce taimakon kai tsaye. Yana nuna hangen nesa mai kyau da kuma kudirin ƙarfafa matasa,” in ji shi.
Musa ya ƙara da cewa ƙungiyar na da yaƙinin cewa Jidda na da ƙwarewar wakiltar mazaɓarsa yadda ya kamata a Majalisar Tarayya ta ƙasa, inda ya buƙaci shugabannin jam’iyyar APC da Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya su yi la’akari da shi wajen ba shi tikitin takara.
Shi ma da yake nasa jawabin, Uzaifa Ali Bigji ya bayyana Jidda a matsayin mutum mai kusanci da jama’a wanda ya dade yana tallafawa al’umma.
“Ba yau ya fara ba. Ya shafe shekaru yana taimakon jama’a a boye,” in ji shi.
Wani mai goyon baya, Babangida Kupto, ya ce farin jinin Jidda na ƙara ƙaruwa har ma ya wuce iyakokin jam’iyya, lamarin da ke sa ya zama ɗan takara mai ƙarfi.
Sauran masu ruwa da tsaki da suka haɗa da sarkin matasan Funakaye, Alhaji Musa Goje, da Hon. Muhammad Ajiya, sun yabawa tsarin Jidda na haɗa kan jama’a, suna mai bayyana shi a matsayin jagora mai iya haɗa kan al’umma.
Jagorar mata ta ƙungiyar, Wunan Anthony, ta ce tsayawarsa takara zai ƙara haɓaka shigar matasa da mata cikin harkokin siyasa.
Masu sharhi na ganin cewa ƙaruwar karɓuwar Jidda, musamman a tsakanin matasa, na iya taka muhimmiyar rawa wajen tsara sakamakon zaɓen fidda gwani na APC yayin da shirye-shiryen siyasa na zaɓen 2027 ke ƙara ɗaukar zafi.
