Daga USMAN KAROFI
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai bar Abuja a ranar Asabar, 2 ga Mayu, domin kai ziyara zuwa Faransa, Kenya da Rwanda. Ziyararsa ta farko za ta kasance a Faransa, kafin daga bisani ya wuce Nairobi na Kenya domin halartar taron Africa-France da aka shirya farawa mako mai zuwa.
Taron wanda Emmanuel Macron da William Ruto ke jagoranta zai mayar da hankali kan sauyin makamashi, masana’antu masu ɗorewa, sauyin fasahar zamani, da kuma gyaran tsarin hada-hadar kuɗi na duniya. Halartar Tinubu daga 11 zuwa 12 ga Mayu zai nuna ƙudirin Najeriya na ƙarfafa dangantaka da ƙasashen Afirka da kuma Faransa, tare da tattauna muhimman batutuwa kamar bunƙasar tattalin arziki, sauyin yanayi, da bunƙasar matasa.
Bayan kammala taron a Kenya, shugaban ƙasar zai tafi Kigali na Rwanda domin halartar taron Africa CEO Forum daga 14 zuwa 15 ga Mayu. Taron na bana mai taken “Scale or Fail” zai haɗa shugabannin kamfanoni, masu zuba jari da masu tsara manufofi domin tattauna hanyoyin bunƙasa tattalin arziki ta hanyar hadin gwiwa da zuba jari tsakanin kasashe. Ana sa ran Tinubu zai gabatar da jawabi kan gyare-gyaren da gwamnatinsa ke yi domin jawo zuba jari, tare da ganawa da manyan shugabannin kasuwanci kafin dawowarsa Najeriya bayan kammala tarukan.
